Mutane 1,170 Mafiya Buƙata a Karamar hukumar Malumfashi sun samu Tallafin Shinkafar Gwamnatin Tarayya

top-news

An gudanar da raba tallafin shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta samar cikin nasara a karamar hukumar Malumfashi, karkashin jagorancin Abdulkadir Mamman Nasir (Andaje), Daraktan Hukumar Raya Noman Rani ta Katsina. An shirya wannan tsari ne domin samar da abinci ga mafiya bukata a cikin al’ummomi daban-daban na jihar.

Mallam Andaje, wanda shi ne shugaban kwamitin rabon tallafin a Malumfashi, ya bayyana tsarin rarraba shinkafar, inda ya ce an bai wa kwamitocin unguwanni amanar rabon tallafin yadda ya kamata. Ya ce, “Mun tabbatar da cewa an hada dukkan masu ruwa da tsaki a cikin wannan tsari, ciki har da kansilan unguwa, dagaci, da kuma wakilan matasa da mata.”

Domin tabbatar da gaskiya da adalci a cikin rabon tallafin, an hada wakilan jam’iyyu daban-daban a cikin wannan tsari. An yi hakan ne don tabbatar da cewa tallafin ya kai ga wadanda suka fi bukata ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ba.

“Mun zaɓi mutane 1,170 bisa ga yadda aka ware wa karamar hukuma. Kowanne daga cikin waɗanda aka zaɓa zai sami buhun shinkafa mai nauyin 25kg wanda zai iya ɗaukar iyali tsawon akalla mako guda,” in ji Abdulkadir Mamman Nasir.

Ya jaddada kalubalen da ake fuskanta wajen cika bukatun dukkan al’umma, amma ya yi nuni da cewa an fi mai da hankali ne kan wadanda suka fi bukata. An fara rarraba tallafin ne daga unguwannin 30 a karamar hukumar Malumfashi, inda aka ware buhunan shinkafa 90 bisa ga yawan rumfunan zabe.

An gudanar da aikin rabon tallafin cikin nasara, inda kansilolin unguwa da kwamitocin su suka kula da tattara da jigilar shinkafar zuwa al’ummominsu. Andaje ya tabbatar da cewa za su ci gaba da kasancewa a wurin rabo har sai dukkanin unguwannin 12 na karamar hukumar sun karbi tallafin su, tare da tabbatar da cewa an fitar da duk kayan tallafi daga rumbun ajiya  kafin yabar wajen. 

Barrister Abdullahi Garba Faskari Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina kuma shugaban kwamitin a shiyyar Funtua wanda Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya mamba a kwamitin ya wakilta, yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya na raba tallafin shinkafa a Malumfashi. Ya ce, “Ba karo na farko bane da nake lura da rabon kayan tallafi a Malumfashi. Tsarin ya kasance yadda ake so kuma yana da kyau, abin a yaba ne.”

Tawagar rabon abincin a yankin Funtua ta kunshi wakilai daga kungiyoyin fararen hula, kungiyar matasa ta Najeriya (NYCN), jami’an tsaro DSS da ‘yan sanda, tare da jami’an gwamnatin jihar Katsina.