Gwamna Radda Yana Ci Gaba da Ziyarar Kasar Sin Don Inganta Tattalin Arzikin Jihar Katsina
- Katsina City News
- 19 Aug, 2024
- 470
A ci gaba da ziyarar kwanaki biyar da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD CON, ke jagoranta a kasar Sin, tawagarsa ta ziyarci kamfanin Jinan Zhongnihaihe ZNH da ke kasar.
Shugaban Kamfanin, Williams Xu, ya yi maraba da tawagar tare da yi musu cikakken bayani game da ayyukan kamfanin a Najeriya. Ya bayyana cewa kamfanin yana samar da manyan motoci, injinan noma, da injinan gine-gine. Kamfanin yana taka muhimmiyar rawa a bangaren motocin tarakta da kuma masana'antu da ayyukan noma a Najeriya.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD CON, ya nuna sha'awar yin hulɗa da kamfanin. Ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce domin tattara bayanai yadda kamfanin zai iya tallafawa bangaren tattalin arziki tare da samar da masana'anta a Jihar Katsina domin inganta kayan aiki da na'urorin da za a samar.
Haka kuma, gwamnan ya bayyana mahimmancin wannan aiki wajen inganta tattalin arzikin jihar da ma al'umma baki ɗaya.
Tawagar ta kuma ci gaba da duba hanyoyin habaka harkokin noma daga kamfanin Shandong Minsheng da kuma yadda za a inganta tashar jirgin kasa ta tudu da ke yankin Funtua. Bugu da ƙari, tawagar za ta ziyarci ɓangarori da ke samar da kayan noman rani ta hanyar zamani da sauran su.
Daga cikin mambobin tawagar akwai Sakatare na Musamman na Gwamna Radda, Malam Abdullahi Aliyu Turaji, Kwamishinan Noma, Kwamishinan Kasuwanci da wasu manyan jami'ai.
Jagorancin wannan tawaga ya nuna ƙoƙarin Gwamna Radda na tabbatar da kyakkyawan tsari da bin diddigi a gwamnatinsa, tare da samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da sauran ƙasashen waje domin ci gaban tattalin arzikin jihar baki ɗaya.