Tinubu ya kori Arabi tare da naɗa Sheikh Saleh Pakistan a matsayin shugaban NAHCON

top-news

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke, Jalal Arabi daga shugabancin hukumar kula da aikin Hajji ta kasa, NAHCON,  tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Usaman, wanda aka fi sani da Sheikh Saleh Pakistan.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Litinin ta ce nadin nasa zai cigaba da aiki har zuwa lokacin da majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

Sanarwar ta ce, shugaban kasar na fatan, Farfesa Saleh zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana.

Idan za a iya tunawa dai, tsohon shugaban hukumar, Jalal Arabi na fuskantar tambayoyi game da zargin badakala a yayin aikin Hajjin 2024.

Jalal Arabi da wasu jami'a NAHCON na amsa tambayoyi a hukumar EFCC da ICPC.

NNPC Advert