Zanga-Zanga: 'Yan Daba Sun Lakadawa 'Yan Jarida Duka, -Sun Lalata Motar NUJ
- Katsina City News
- 31 Jul, 2024
- 326
Gabanin fara Gudanar da zanga-zangar jama'a a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta, 2024, 'yan daba a Calabar, babban birnin jihar Cross River, sun dira kan 'yan jaridu, inda suka raunata daya daga cikinsu wanda ya kasance wakilin jaridar Nigerian Tribune, Joseph Abasi-Abasi ne.
‘Yan dabar sun kuma lalata wata motar NUJ mai kujeru 18 da ke jigilar kayan abinci daga rumbun ajiyar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar zuwa Cibiyar 'yan Jarida ta Ernest Etim da ke Calabar.
Sun kuma lakada wa direban bas din NUJ, Mista Joseph Akpaenin, da ma’aikacin NUJ, Mista Savior Ekpenyong duka.
Kayan Tallafin ya kasance na kungiyar ‘yan jarida (NUJ) majalisar jihar Cross River ne.
Bayan lakadawa ‘yan jaridar duka, sun yi nasarar kwashe wasu kayan abinci daga cikin motar.
Direban bas din, Joseph Akpaenin, wanda shi ma aka sace wayarsa, an bar shi da duka a kafada da fuska daga harin.
Abun takaici wasu 'yan jarida sun sami raunuka masu yawa a ya yin harin .
Shugaban kungiyar NUJ a jihar, Comrade Archibong Bassey ya yi Allah wadai da wannan aika aika.