"Kalu-balen da na Fuskanta a wajen Boko Haram" - Hajiya Bilkisu Babangida, Tsohuwar Ma’aikaciyar BBC Hausa
- Katsina City News
- 19 Jul, 2024
- 436
Babu shakka na hadu da kalubale a rayuwa, mafi girma daga cikin su shi ne lokacin da na samu kaina tsakanin hukumomi da kuma mayakan Boko Haram a yayin gudanar da aikina, musamman ma shekara daya bayan yakin Boko Haram, a lokacin da suka sake dawowa bayan cin galabar da jami'an tsaro suka samu a kansu. Sun sake dawowa garin Maiduguri don daukar fansa, inda suka fara kai harin sari-ka-noke kan 'yan sanda da Bulamomi da Lawanai kai har ma da wasu malaman addini da kuma daidaikun mutane.
Sai dai lokacin ba ma a fahimci ko su wanene suke aikatawa ba, sai kawai a ga ana ta kashe dan sanda, ana dauke bindigarsa, wanda a lokacin wani sabbon abu ne. A duk lokacin da aka yi kisan nakan rika daukar rahotanni, wani lokaci ma ba a dauke gawar ba za a gan ni a wurin. Ana nan kwatsam wata rana da daddare sai na ji wayata ta buga, amma an rufe lamba sai na dauka na ce, don Allah da wa nake magana don na fi son in rika ganin lamba, sai kawai na ji an ce, ki saurare mu da kyau, muna so nan da kwanaki kadan za mu bugo kuma za mu bude lambar don muna so mu bayyana dalilan da ya sa muka dawo muna kashe-kashe a cikin Maiduguri. Daga nan ne na fahimci ko su wane ne.
Na jira bayan kwanaki sai aka sake kirawo ni da tsakar dare, sai mutumin ya ce min to yanzu mun shirya fada wa duniya dalilan da suka sa muke aikata abin da muke aikatawa. Muka kammala hira, to dama tun kafin lokacin na shaida wa Shugabar Sashen Hausa na BBC a wancan lokaci, Jamila Tangaza, inda ta ba ni shawarwari kan yadda zan tunkari abin. Washegari aka saka hirar kuwa, inda daga nan ne muka fara takun-saka da hukumomi da suka hada da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) a jihar, wanda sun sha kira na don amsa tambayoyi kan yadda aka yi nake magana da 'yan Boko Haram. Nakan ba su amsar cewa, kamar yadda sauran masu sauraren mu ke da lambobina, su ma hakan ne, ni ban taba sanin fuskokinsu ba. Haka dai aka rika sa-ido a kaina, kuma da na fita aiki za ka ga ana dari-dari da ni.
Akwai kuma lokacin da 'yan Boko Haram din suka taba kira na a waya cewa, shugabansu, Shekau zai yi wasu maganganu game da abubuwan da jamaa ke son ji a kan dalilan da suka sa suke kaddamar da hare-harensu, saboda haka tun da ni 'yar jarida ce, suna son in tura da duk wasu tambayoyi da jamaa ke yi game da su don ya ba su amsa. Na tura musu da tambayoyin bayan kwanaki kadan sai kawai na ji kira ta wayata, inda wani a cikinsu ya ce min, "Imam ya kammala nadar hirar kuma a ina za mu same ki, mu kawo miki memory card din? Daga nan, ya ce ga hirar da Imam ya yi, aka ce mu kawo miki. Sai na ce to kun san kamar yadda aikin yake, akwai na gaba da ni, idan na saurara zan tura musu. Muna cikin magana da su sai ga wani sanye da farar babbar riga aska biyu ya shigo. Shigowarsa ke da wuya, sai suka mike tsaye, suka fita waje, shi kuma ya zauna. Sai ya ce min sunansa Abu Fatima, sai na fahimci yana daya daga cikin 'yan Boko Haram din da suka saba kira na, kuma shi ya taba tabbatar min da harin da suka kai a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja. Daga nan sai ya kara jaddada min batun memory card. Shi ma sai na bayyana masa irin abin da na fada musu, ya ce ba damuwa, sai suka kama hanya suka tafi. A ranar cikin dare sai suka kira, suka ce, sun fada wa Imam duk yadda muka yi, ya ce Allah Ya yi albarka. Kuma inda Allah Ya taimake ni, na fada musu gaskiyar cewa ina da na gaba, don kada su ji ba a yi amfani da hirar ba.
Daga jaridar Aminiya