Tatsuniya Ta 35: Labarin Wata Mata Da Ya’yanta

top-news

Ga ta nan, ga ta nanku. 

A can kudu da garin su Gizo da Koki akwai wata mace mai 'ya'ya mata su hudu, waɗanda ubansu daya ne. Suna nan zaune cikin jin daɗi, sai ciwo ya kama mijinta, watau uban yaran nan. Da ya ga kamar ba zai tashi ba, sai ya sa aka yi wa 'yan matan nan hudu aure. Bayan wata uku da aurar da su, sai ya cika.

Daya daga cikin 'ya'yan nan ta yi aure a garin da ba a barci; ta biyu ta yi aure a garin da ake tsinkar gauta da hanci da tsinkar kubewa da kirji; ta uku kuma ta yi aure a garin da ba a cin abinci, ba a kashi sai dai a sha romon nama; ta hudun ta yi aure a garin da ba a kwana a gida sai a can sararin sa

Ziyarar Matar ga 'Ya'yantaZiyarar Ta Farko: Garin Da Ba a Barci

Wata rana sai matar ta shirya za ta ziyarci 'ya'yanta. Ta fara zuwa garin 'yarta ta fari, watau garin da ba a barci. Da ta je gidan 'yarta, sai 'yar ta razana ta ce: “Inna me ya kawo ki garin nan da ba a yin barci?" Tun da tana son ganin diyarta, sai ta ce mata: "Ai tun da babanku ya rasu ban sake barci ba." Sai 'yar ta ce: "To shi ke nan."

Suka zauna ta yi mata abinci ta ci. Da dare ya yi sai suka kama hira a cikin daki. Can sai uwar ta fara gyangyadi. Da 'yar ta ga haka, sai ta ce da ita: "Kada ki yi barci fa." Sai ta juya suka ci gaba da hirarsu da mijinta. Jiki da jini, can sai uwar ta kwanta ta kama barci. Da mijin 'yar ya lura surukarsa ta kwanta tana barci, sai ya fita ya tara mutane ya ce surukarsa ta rasu.

Da gari ya waye, sai masu haka kabari suka tafi makabarta suka kama aiki. Aka shiga shirye-shiryen binne wannan matar. Da ta ji hayaniyar mutane, sai ta fito tana yi musu magana, tana cewa ita fa ba ta mutu ba, barci kurum ta yi. To su ba su san barci ba. Sai wani daga cikin mutanen da suka taru ya ce wa sauran da ke saurarenta: "Yaya kuke magana da fatalwa bayan kun san ta mutu? Mutum zai mutu ya dawo ne?"

Wannan abu ya tsorata matar, saboda haka sai ta koma cikin dakin 'yarta; sai 'yarta ta ce: "To kin san na gaya miki ba a barci a nan garin; su ba su san barci ba." Bakuwar nan ta rasa yadda za ta yi. Idanu suka raina fata. Can dai wata dabara ta fado wa 'yar. Ta dubi uwar ta ce: "Zo in fitar da ke ta danga ki gudu, in ba haka ba za su binne ki da rai." Sai ta ja ta suka bi ta bayan gida, ta bude mata hanya ta gudu ta nufi garinsu.

Ziyarar Ta Biyu: Garin Da Ake Tsinkar Gauta da Hanci da Kubewa da Kirji

Bayan kwana daya da komawar matar nan gida, sai ta ce bari ta je garin 'yarta ta biyu, watau garin da ake tsinkar gauta da hanci kuma a tsinka kubewa da kirji. Sai ta kama hanya har ta isa garin. Da ta isa gidan 'yar, sai 'yar ta ce: "Inna me ya kawo ki nan? Kin sani fa a nan garin ba a cin abinci. Kowa sai dai ya tsinki kubewa da kirji, kuma ya tsinki gauta da hanci. Shi ne kawai abin da mukan ci. Idan kuma ba ki tsinka ba, to kuwa ba za kici komai ba."

Da jin haka sai uwar ta ce: "Haba, ai mu ma a garinmu da kirji muke tsinkar kubewa, sai da na auri babanku na daina." Sai 'yar ta ce: "To shi ke nan."

Da yamma ta yi, duk sauran matan gida suka dunguma gona tsinkar kubewa tare da bakuwar. Kowa ya kama yana tsinka, har suka koshi. Amma bakuwar nan ba ta tsinka ba, ƙirjinta ko ya dame ta da kaikayi. Haka ta kwana da yunwa. Washe-gari ma kowa ya tsinka kubewa da gauta da ƙirjinsa, amma ban da ita. Ta sake kwana da yunwa. Da ta ga ta kwana biyu ba ta ci komai ba, sai ta gaya wa 'yarta za ta koma gida. Da 'yarta ta ji haka, sai ta dubi uwar ta ce: "To, bari in raka ki."

Sai ta riƙe wa uwarta kwaryarta ta raka ta bayan gari, suka yi bankwana, kowa ya koma garin da yake.

 Ziyarar Ta Uku: Garin Da Ba a Cin Abinci sai Romo

Da matar nan ta isa gida ta huta kwana daya, sai ta shirya ziyartar 'yarta ta uku, watau dai ba ta daddara ba. 'Yar kuwa tana can garin da ba a cin nama sai dai romo, domin su zubar da nama suke yi idan sun dafa. Sai ta haɗa kayanta, ta kama hanya sai garin 'yarta ta uku. Da ta isa sai 'yar ta yi mamakin ganinta, kuma ta ce da ita: "Inna ba za ki iya zama a nan garin ba saboda a nan ba a cin abinci, ba a yin kashi, kuma ba a cin nama sai dai romon naman."

To abin ka da wanda ya saba da gardama, sai uwar ta ce: "Haba, ai ni na daina cin abinci tun sanda babanku ya mutu."

Da ta ji bayanin uwar sai ta ce: "To shi ke nan."

Sai suka zauna. Da lokacin cin abinci ya yi, sai ta ga 'yarta ta dafa nama mai yawa, ta tsiyaye romon, za ta zubar da naman, sai ta ce: "Haba 'yar nan ai kin gaji, bari in je in zubar miki da shi." Da ta karɓi nama ta fita bayan gida sai ta zauna ta cinye shi duka.

Bayan ta dawo sai 'yar ta tambaye ta: "Yaya na ga kin daɗe ba ki dawo ba?" Da uwar ta ji wannan tambaya sai ta ce: “Ai bayan gari na kai."

Sai 'yar ta ce: "To madalla, hakan ya yi."

Can cikin dare sai uwar ta tashi daga barci ta ce wa 'yarta tana jin kashi. Sai 'yar ta ce mata: "Ki tuna fa na gaya miki ba a yin kashi a nan garin, shi ya sa ma ba mu da shadda a nan garin." Da kashin ya matsanta wa uwar, sai 'yar ta ba ta tukunya ta cika ta da kashi; 'yar kuma ta boye tukunyar kashin.

Da gari ya waye sai kajin garin suka kama cara da kuka suna cewa: "Kukuruku, an yi kashi a garin nan." Idan akuya ma za ta yi kuka sai ta ce: “Be, be, be, an yi kashi a garin nan." Haka dai duk dabbobi suka dinga yin wannan fallasa a cikin kukansu. Da abin ya yi yawa sai Sarkin garin ya tara mutanen garin ya ce: "Wane ne ya yi kashi a garin nan?"

Kowa ya ce bai sani ba. Aka yi ta bincike, kowa yana cewa bai yi kashi ba, kuma ba su san wanda ya yi ba. Da Sarki ya ga magana tana nema ta yi tsawo, sai ya ce: "To za a yi al'adar da aka saba yadda duburar duk wanda ya yi kashin nan za ta rika waka, kowa ya ji a gari."

Sarki ya sa aka yi magani; nan take duburar matar nan ta fara waka. Da yar ta ji sai ta ce: “Inna zo in raka ki domin kada a sani mu ji kunya." Nan da nan cikin gaggawa ta tattara kayanta, ta raka ta bakin gari suka yi bankwana ta tafi bayanta na waka.

Matar nan tana cikin tafiya a dajin da ke tsakanin garin da ta je da wanda za ta, sai ta haɗu da wani Bafulani yana kiwo; sai ya ce yana son jin wannan waka mai daɗi haka. Sai ta ce: "Zan ba ka idan za ka ba ni shanu biyu." Kamar da wasa sai ya amince da hakan. Ta ce masa ya yi kashi ya shafa mata, abin zai koma ikinsa. Sai ya ba ta shanu biyu, kuma ya yi kashi ya dangwala ya shafa mata. A nan take abin ya koma jikinsa, yana waka. Da ya shiga daji da shanunsa yana murna. Ita kuwa ta kora shanunta biyu ta shiga gari, ta je gida ta daure kayanta