A YAU LAHADI: YAN BINDIGA SUN KAI MA MANOMA HARI A GARURUWA DA GONAKI A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 30 Jun, 2024
- 489
Abdullahi Abdussamad @Katsina Times
Ƴan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa na ci gaba da yin kisa da ɗaukar manoma a yankin Batsari ta jihar Katsina.
A ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, 2024, da rana tsaka, ƴan bindiga sun fantsama cikin karkarar wasu yankunan Batsari, inda suka farmaki wasu manoma a gonakansu dake ƙauyen Ɗangeza, suka kama mutane biyar.
Haka kuma, a ƙauyen Batsarin'alhaji, sun kama manoma biyu, sun yi awon gaba da su. Duk a ranar ta Lahadi, sannan sun kwace shanu huɗu a yankin Yasore.
A ƙauyen Nahuta kuma, sun samu mutane na aiki a gonakansu, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi suka kashe mutum ɗaya mai suna Malam Garba, wanda dama baa daɗe da karɓo shi ba daga hannun masu garkuwa da mutane bayan an biya kuɗin fansa. Sannan a makon da ya gabata, sun yi wa wani manomi harbi uku akan hanyarshi ta dawowa daga gona a ƙauyen Nahuta.
A wani labarin, ɓarayin daji sun kai hari ƙauyen Watangaɗiya ta Batsari da misalin 12:00 na tsakiyar daren ranar Alhamis, wayewar garin Jumma'a, 28 ga watan Yuni, 2024, inda suka ɗauki shanu huɗu da babura biyu.
Wannan yanayi yana neman zama jiki ga al'ummar wannan yanki, domin kwanakin baya ɓarayin sun kashe mutane biyu a gonakansu dake ƙauyen Batsarin'alhaji lokacinda suke tsaka da aiki. Ya zuwa rubuta rahoton nan, bamu samu wani bayani daga jami'an 'yan sanda ba. Amma mutanen yankunan sun tabbatar mana da faruwar lamarin.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.taskarlabarai.com
All on Our social media platforms