'Ya'yan Jam'iyyar PDP sun koka akan rashin fara saida Fom din takara a Katsina
- Katsina City News
- 19 Jun, 2024
- 468
Aƙalla kananan hukumomi shida daga Jihar Katsina, tare da jagororin jam'iyyar PDP na jihar, sun je sayen fom din tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar amma sun taras babu kowa a helkwatar jam'iyyar.
Alhaji Salisu Uli, wanda ya jagoranci wannan ziyara, ya bayyana cewa sun ziyarci helkwatar jam'iyyar PDP dake kan hanyar Kano a cikin garin Katsina domin sayen fom din tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar a matakai daban-daban. Duk da sanarwar da uwar jam'iyyar PDP ta bayar na fara saida fom din, babu kowa a helkwatar, ofisoshin kuma garkame.
Uli ya nuna rashin jin dadin ganin babu mai saida fom din duk da cewa lokacin yana kara kurewa. Ya ce an ba da sanarwar fara saida fom din daga ranar uku ga Yuli, amma har yanzu babu wani tsari a helkwatar jam'iyyar ta jihar Katsina.
Kananan hukumomin da suka halarci ziyarar sun hada da Kankiya, Mashi, Danmusa, Katsina, Funtua, da Malumfashi. Wakilan jam'iyyar sun bayyana damuwar su kan rashin samun fom din a cikin lokaci, suna masu cewa za su ci gaba da bincike kafin wa'adin rufe saida fom din ya kare nan da kwana biyar.