Zamfara: Gwamna Dauda Lawal Ya Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi na Naira Dubu 30
- Katsina City News
- 16 Jun, 2024
- 457
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikatan Jihar, tare da biyan albashin watan Yuni saboda shagalin Babbar Sallah.
A watan da ya gabata ne gwamnan ya shaida wa shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Zamfara cewa zai fara biyan mafi ƙarancin albashi a watan Yuni.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Gusau, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa ma’aikatan jihar Zamfara sun fara karɓar albashinsu ne a ranar 12 ga watan Yuni, gabanin bikin Babbar Sallah.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi, wanda hakan ya bayyana a cikin albashin watan Yuni da ta riga ta biya.
“Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta biya albashin watan Yuni domin tallafa wa ma’aikata a shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.
“Wannan ya yi daidai da cika alƙawarin da gwamnan ya yi a watan jiya na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30.
“Kafin yanzu, ma’aikatan gwamnati a Zamfara na karɓar mafi ƙarancin albashin Naira dubu bakwai ne kacal.
“Gwamnatin Dauda Lawal ta kasance mai son ma’aikata tun lokacin da aka kafa ta, inda ta tabbatar da biyan albashin watanni uku da aka hana su, kuɗaɗen hutu, basussuka, da biyan albashi a kan kari.
“Gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin kawo gyara da kuma farfaɗo da ma’aikatan jihar Zamfara,” in ji sanarwar.