Babbar Magana: Gwamnatin Yobe Ta Sauke Kur'ani Tare Da Yanka Dabbobi Kan Masu Lalata Wutar Lantarki A Tsakanin Yobe Da Borno
- Katsina City News
- 16 May, 2024
- 662
Yau laraba, 15t ga Mayu, 2024, bayan Gwamnatinsa ta kammala gyaran turankun (towers)) wutan lantarki na 330KVA wanda wasu ba a san su wanene ba suka lalata a watan Febrairu na wannan shekarar a kusa da kauyen Kasaisa, Gwamnatin Mai Mala Buni, CON, Buni ta jagoranci ɗaga Al-Qur'ani akan masu lalata wutar lantarkin domin dawo da wutan lantarki a yankunan Yobe da Borno.
Kwanakin baya Mai girma Gwamna ya sha alwashin daga Al-qur'ani akan masu wannan mummunan aikin bayan ya bayyana damuwar sa akan irin wahalhalun da mutanen Jihar Yobe suke fama da su na rashin wutan lantarki da ruwan sha Mai girma Gwamna yayi magana cikin bacin rai har yace Gwamnatinsa baza ta aminta da duk wata shirin da zata jefa mutanen Jihar Yobe cikin wahala ba.
Idan bamu manta ba, kamar yadda kamfanin raba wutan lantarki na Yola Electricity Distribution Company (YEDC) ta bayyana, a watan disemba na shekarar 2023 ne aka fara lalata layukan wutan lantarkin a kusa da kauyen Kasaisa dake kan hanyar Gujba,
Gwamnatin Mai Mala Buni ta kashe makuɗan kuɗaɗe ta gyara su. Haka zalika, a watan febwari na shekarar 2024 aka sake lalata wasu, har ila yau Gwamnatinsa ta sake kashe makuɗan kuɗaɗe ta gyara domin damuwa da rayuwar mutanen Jihar Yobe.
Yau a wajen taron ɗaga Al-Qur'anin, an gayyato manya-manyan Malamai da Almajirai daga sassa daban-daban, an yanka shanaye (zubar da jini) anyi karatun Al-Qur'anin mai girma kuma anyi addu'an Allah ya tona asirin (duniya da lahira) wasu mutane kamar haka:
i. masu aikata aikin lalata wutan lantarkin,
ii. masu ɗaukan nauyin su,
iii. masu taimaka musu,
iv. masu basu kayan aiki,
v. masu basu bayanan sirri,
vi. masu haɗa baki da su,
vii. Duk wanda sun san su basu fallasa su ba,
viii. Da wanda yake kaisu,
ix . Da wanda yake sayan kayan da aka sata,
x. masu sarauta, ma'aikatan Gwamnati ko ma'aikatan kamfanin wutan lantarki,
xii masu sace kayan transformer a Jihar Yobe.
Taron wanda akayi shi karkashin kananan hukumonin Gujba, Damaturu da Gulani ta samu halartan mai bawa Gwamna shawara akan harkan tsaro Gen. Dahiru Abdulsalam da mai bawa Gwamna shawara akan harkokin addini Ustaz Babagana Mallam Kyari.
Daga karshe, muna sa ran insha Allah cikin kwanakin nan mutanen Jihar Yobe zasu cigaba da moran wutan lantarki kamar yadda suke a baya kasancewar Gwamnatin Mai Mala Buni ta gyara layukan wutan lantarkin da aka lalata,
Haka zalika kamfanin rarraba wutan lantarkin Najeria ta bayyana cewa tana daf da kammala gyaran hasumiyai har guda hudu da aka lalata a kan layin Jos-Gombe.