Gwamnatin Tarayya Ba Ta Tunanin Kafa Sansanonin Sojojin Kasashen Waje A Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Katsina City News
- 07 May, 2024
- 506
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba ta tunanin kafa sansanonin soji na ƙasashen waje a Nijeriya.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Litinin, Idris ya bayyana rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa a matsayin ƙarya.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin haɗin gwiwar soja da wasu ƙasashe kuma ta na son zurfafa shi domin cimma manufofin tsaron ƙasa na gwamnatin Tinubu.
Ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta na sane da ƙarairayin da ake ta yaɗawa a wasu wurare na zargin wai ana tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da wasu ƙasashen ƙetare kan batun kafa sansanonin sojojin ƙasashen waje a ƙasar.
“Mu na kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙarya gaba ɗaya.
“Gwamnatin Tarayya ba ta irin wannan tattaunawar da wata ƙasar waje. Ba mu samu ba kuma ba mu yi la’akari da wata shawara daga wata ƙasa ba game da kafa sansanonin sojin ƙasashen waje a Nijeriya.
“Gwamnatin Nijeriya ta riga ta ba da umarnin haɗin gwiwa da ƙasashen waje wajen tunkarar matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta, kuma Shugaban Ƙasa ya jajirce wajen zurfafa wannan ƙawance, da nufin cimma manufofin tsaron ƙasa na Ajandar Sabunta Fata.” inji shi.