ƁARAYIN DAJI SUN KAI TAGWAYEN HARE HARE A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 04 May, 2024
- 514
Daga Misbahu Ahmad
@ Katsina Times
Ɓarayin daji sun kai tagwayen hare hare a ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
A daren ranar alhamis 02-05-2024, ɓarayin suka kai hari ƙauyen Sakijiki mai nisan 5km daga garin Batsari, inda suka kashe mutum ɗaya kuma suka yi garkuwa da wani mutum ɗaya. Lamarin ya faru da misalin 01:00am, yayin da wani ɗan sintiri ya mai suna Kabir Abdullahi ya dawo daga aikin bada tsaro, yana ɗauke da bindigarshi, sai ya iske wasu mutane suna ƙoƙarin kama wani mutum su tafi da shi, amma ya zaci ko abokan aikinsa ne, sai ɓarayin suka saki mutumin, suka ce kai sajen ga ɗan banga nan, jin haka ke da wuya sai ɓarawon da ke da bindiga daga cikin ɓarayin ya buɗe masa wuta ba ƙaƙƙautawa ya kashe shi. Sannan suka tafi da wani Abdullahi Ashiru dake kwance a waje domin shan iska.
Haka ma a Garinkarɓau dake kusa da Wagini duk cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari, ɓarayin sun kai hari ranar laraba da dare 01-05-2024, inda suka kashe mutum biyu suka yi garkuwa da mutane uku.
Matsalar tsaro ba sabon al'amari ba ne a yankin Batsari domin ko cikin makon da ya gabata ɓarayin na daji sun sace mutane huɗu a gonakansu dake ƙauyen Nahuta.