Maganar da Bashir Ahmad Yayi Akan Aikin Hanyar Kano-Katsina Bai Faɗi Gaskiya Ba - Al-Amin Isa
- Katsina City News
- 28 Apr, 2024
- 367
Na karanta wani Rahoto da Muhammad Aminu Kabir ya wallafa a shafinsa akan aikin hanyar Kano zuwa Katsina inda yace Tsohon Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman akan Kafafen Sadarwa na Zamani yace rashin kammala aikin hanyar Kano zuwa Katsina laifin Gwamnatin Katsina ne.
Inaga ko dai Bashir Ahmad yayi maganar ne amma baisan ainahin cikakken bayanin ba ko kuma yayi ne domin yaɓata tsohuwar Gwamnatin tunda mutane basu san ainahi sahihin labarin ba, kuma yanzun basa kan mulki. Tunda Bashir Ahmad yafara magana to lokaci yayi da zamu mufito muyiwa jama’a wasu bayanai da ada mukayi shiru bamuyi ba, domin su san irin yadda Gwamnatin Buhari ta rinƙa siyasantar da dukk wani aiki daya shafi Jihohin Arewa kana mutanenmu ʼyan Arewa dake majalisar zartaswa ta Gwamnatin Buhari a lokacin suka kasa tsayawa sukare yankin namu don wasu dalilai nasu nason zuciya.
Shi wannan aikin Gwamnatin marigayi Malam Umaru Yar’adua ta assasa shi, kuma aka raba shi kashi nafarko (1) zai taso daga cikin Kano yatsaya border ta Kano da Katsina. Kashi ba biyu (2) zai tashi daga border din Kano da Katsina zuwa cikin Katsina. Aikin nan tun wanchan zamanin akeyinshi yarinƙa tafiyar Hawainiya har zuwan Gwamnatin Buhari tagaje shi daga Gwamnatin GEJ. Shi kanshi aikin Jihar Kano ɗin ba’a kammala shi ba aka fara kashi na biyu (2) cikin Jihar Katsina.
Gakiyar lamari shine kowa yasan cewar dukk inda Gwamnatin Tarayya ke aiki hakƙinta ne biyan diyyar dukk wuraren da za’ayi aikin. Bayan da Gwamnatin tazo Gwamnan Jihar Katsina yayi magana da Ministan Ayyuka na Ƙasa Farfesa Fashola cewar Jihar Katsina na da buƙatar Gwamnatin Tarayya tayi musu wasu ayyuka, Fashola yabuƙaci Gwamna yatura Kwamishina na Ayyuka lokacin Inginiya Tasi’u Ɗandagoro yakawo mashi dukk bukatun. Kwamishina yaje Abuja da bukatu cikin bukatun akwai hanya data tashi daga Zaria ta ratsa Funtua har zuwa iyakarmu da Jihar Zamfara, akwai hanyar datashi daga Zaria ta ratso ta Hunkuyi wadda ta shigo ta Dabai, Ƙafur zuwa Malumfashi, sai hanya data tashi daga Kano-Kazaure-Daura-Mai’Adua, sai kuma hanyar Kano- Katsina, Sai Hanyar Kano-Gwarzo ta ƙare Dayi. Har yanzun danake magana babu wanda Gwamnatin Buhari ta kammala cikinsu.
Shi wannan aikin na Kano-Katsina Gwamnatin Buhari gadarshi tayi. Kuma cikin ayyukan da Gwamnatin Katsina ta buƙaci ayi mata sai aka ware hanyar Zaria-Hunkuyi-Danja-Dabai-Ƙafur-Malumfashi suka ce ba zasuyi ba domin Gwamnatin Tarayya ta barma Gwamnatin Jiha wannan hanyar. Wannan shine siyasar farko da Fashola yafara yiwa Jihohin Arewa. Ita kuma Gwamnatin Jiha tace babu wata takarda da Gwamnatin Tarayya ta turo mata cewar yanzun wannan hanyar tazama mallakin ta kafin wannan lokacin.
Bayan da aka tura waɗannan bukatun abinda Minista Fashola yayi shine sai da yagama bada approval na biyan Diyya a dukk ayyukan da Gwamnatin Buhari zatayi da waɗanda yagada a Jihohin Kudu waɗanda dayake so, sai yarubutawa Majalisar Zartaswa ta Gwamnatin Buhari cewa Gwamnati ta daina biyan Diyya a dukk ayyukan dazatayi a Jihohi. Baiyi wannan ba sai bayan da yariga yagama biyan dukk wata Diyya a Jihohin Kudu sauran Jihohin Arewa. Ministocinmu ʼyan Arewa batare da tsayawa su tambayeshi yakawo pending ayyuka waɗanda yarage a biya diyya ba, wanda da sunyi hakan zasu ga gaba ɗaya ayyukan Kudu an biyasu na Arewa ne kawai ba’a biya ba, nan zasu gane siyasar da Fashola yakeson yi. Sai kawai suka amince da wannan ƙudurin na Fashola.
Gwamnatin Yar’adua data fara yin aikin bata sanya biyan Diyya cikin conditions nayin aikin hanyar ba ga Jihohin. Jihar Kano kuma basu fidda kuɗinsu ba suka biya Diyya akan aikin da akayi a cikin Jihar tasu ba kamar yadda shi Bashir yayi iƙirari. Abinda yafaru shine lokacin da akazo contract variation sai aka cusha kuɗin biyan diyyar aikin Jihar Kano cikin viriation din na phase 1 aka biya sai da akazo kan na Katsina wanda ke phase 2 sai aka bukaci Gwamnatin Katsina ta biya Naira Biliyan Ɗaya da Dubu Dari Tara da Chasa’in da Huɗu (1.94 Billion) kuɗin Diyya da za’a biya, anan ne Gwamnatin Katsina tace ba zata biya ba sai suma ayi musu dubara yadda akayi aka taimaki Jihar Kano. Minista Fashola yaƙi yadda yayima Katsina hakan shine taƙaddamar data faru. Amma Gwamnatin Jihar Kano ko Kwabo bata fidda daga aljihunta ba tabiya diyya, Gwamnatin Buhari ita ta biya diyyar lokacin da akayi virament domin a idar da aikin phase 1 nasu, dukk da sunyi doka cewar ba zasu sake biyan diyya ba saidai Jihohi su biya.
Ina Ƙalubalantar Bashir Ahmad daya fito yayima jama’a bayani suji shin nawa ita Jihar Kano ta biya diyyar dayace ta biya akan aikin hanyar? Kuma yakawo hujja gamsarshiya da mutane zasu tabbatar Kuɗin Gwamnatin Jihar Kano ne aka biya diyya dasu. Miyasa kuma dukk da an biya diyyar amma har yanzun an kasa kammala masu nasu aikin a ɓaryan cikin Jihar Kano ɗin? Yabamu bayani miyasa Jihar Kano aka taimakesu aka biya masu diyya sai Jihar Katsina akace ita ta biya nata kuɗin kafin ayi mata aikin? Kana inason yayiwa jama’a bayanin miyasa aikin hanyar Kano-Jigawa-Katsina wanda yaratsa ta Daura yaƙare a Mai-Adua wanda yafi nisan Kano-Katsina shima aka biya tashi diyyar ba’a nemi Gwamnatocin Kano-Jigawa-Katsina su biya diyya ba? Bayan akwai doka da ita Gwamnatin Buhari tayi kan biyan Diyya. Ya kuma yi bayanin dalilin dayasa tun cikin shekarar 2016 da Gwamnatin Katsina ta miƙa bukatar ayyukan babu wanda aka gama har Gwamnatin ta tafi bayan Jihohin Kudu dukk anyi musu nasu.
Ina neman bayani daga wurinshi miye dalilin dayasa Gwamnatin Tarayya da ta assasa aikin Jirgin Ƙasa daga Kano yashigo Jigawa yaratso ta Daura zuwa Katsina zai tsaya Maradi a cikin Jumhuriyar Nijar ba’a ce Jihohin su biya Diyya ba? Tunda akwai doka sun kafa Gwamnatin Tarayya ba zata sake biyan Diyya ba?
Kamar yadda Bashir Ahmad yake Tsohon Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman akan Kafafen Sadarwa na Zamani, haka nima nake Tsohon Darakta-Janar na Kafafen Sadarwa na Zamani na Gwamnatin Masari, shiyasa nake mayar mashi da martani domin nasan abinda yafaru. Ina jiran martani daga Bashir Ahmad sai mu dasa daga nan.