NAƊIN SARAUTAR DA SARKIN KATSINA ABUBAKAR YA YI NA ƘARSHE A SHEKARA TA 1904.
- Katsina City News
- 24 Mar, 2024
- 877
A rana irin mai kamar ta yau ne 25/3/1904 sarkin Katsina Abubakar ya yi naɗin sarautar sa na ƙarshe, inda ya naɗa Mayana Ahmadu Rufa'i a fadarsa dake gidan sarkin Katsina.
Mayana Ahmadu Rufa'i ya kasance ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautu da suka rage waɗanda ba'a cire daga sarauta ba tun bayan tafiya da sarkin Katsina Abubakar ɗaurin Talala da Turawan mulkin mallaka su kayi.
Mayana Ahmadu Rufa'i ya yi Wannan sarauta a matsayin Hakimin Koɗa tun daga shekara ta 1904-1919
A shekara ta 1919 ne wani saɓanin rashin fahimtar juna ya shiga tsakanin sarki Dikko da mayana Ahmadu Rufa'i, inda ya ajiye sarautar da kansa ya yi murabus.
Amma duk da haka sarki Dikko har ya gama mulkinsa bai naɗa wani wannan sarauta ta mayana ba har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Haka da ɗan sa Usman Nagogo ya zama sarki bai ba wani wannan sarauta ba, har Allah ya ɗauki rayuwar mayana Ahmadu Rufa'i a shekara ta 1957.
Mayana Ahmadu Rufa'i ya kasance ɗa ne ga machika Abdu Dogo ɗan Sarkin Katsina Ibrahim ɗan Sarkin Katsina Muhammadu Bello ɗan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje.
Mahaifinsa jikan sarkin musulmi Muhammadu Bello ne ta wajen mahaifiyarsa, shiyasa wasu suke ganin ko wannan dalilin ne yasa aka ƙi naɗa wani wannan sarauta, saboda alaƙar da mayana Ahmadu Rufa'i yake da ita da gidan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Ita wannan sarauta ta mayana an fara yin ta tun lokacin Sarakunan Haɓe a Katsina, inda ake naɗa wasu daga cikin ya'yan sarakunan na Katsina.
HAƁE
1. Mayana Ibrahim maje ya taɓa zama sarkin Katsina
2. Mayana Ɗan Tuttubiri ba'a samu cikakken sunan sa ba da shekarun da su kai sarauta.
FULANI
3. Mayana Hassan ɗan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje 1821-1840
4. Mayana Sada ɗan Bebeji Giɗaɗo 1841-1856
5. Mayana Ibrahim ɗan mayana Hassan 1856-1888
6. Mayana muhammadu Sani ɗan sarki Abubakar 1888-1904
7. Mayana Ahmadu Rufa'i ɗan machika Abdu Dogo 1904-1919.
Wannan shi ne jerin sunayen mutanen da su kayi sarautar mayana a Katsina.
Sai lokacin sarkin Katsina Muhammadu Kabir ne aka sa ke farfaɗo da wannan sarauta, inda aka naɗa Alh Abdulƙadir Idris Faskari.
Koda yake wannan sarauta har yanzu ana yin ta a garin koɗa a matsayin magaji ƙarƙashin Hakimin Charanchi.
Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya yasa suna Aljanna maɗaukakiya.
Zaharaddeen Ibrahim Katsina Mayanan Safana