Masu garkuwa da Mutane sun kai hari a garin Mairuwa jihar Katsina sun kashe mutane
- Katsina City News
- 23 Mar, 2024
- 701
Yan bindiga sun shiga garin Mairua sun kashe babban mutum mai suna Alh Lado Mairua da wani makwabcinsa
A labarin dake zo wa Katsina Daily News da Magaribar nan yan bindiga sun shiga garin Mairua yankin ƙaramar hukumar Faskari, inda suka durfafi gidan Alh Lado Mairua, wanda babban mutum ne kuma shahararre a yankin, inda suka kashe shi suna cikin sallar tarawi tare da wani makwabcinsa mai suna Sani Autan Haris
Daya daga cikin 'ya'yan marigayin ne ya tabbatar wa Katsina Daily News faruwar lamarin, inda yana magana cikin kuka yana cewa "Sun kashe man ubana da makwabcinmu"
Yankin ƙaramar hukumar Faskari na daya daga cikin manyan yankuna dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina, inda da wuya a yi kwana ɗaya ba a sami rahoton yan bindiga sun kai hari a wasu garuruwan yankin ba.