YADDA ATTAJIRAI 'YAN ASALIN NIJAR MAZAUNA NAJERIYA KE TALLAFAWA KASAR SU
- Katsina City News
- 16 Feb, 2024
- 619
Muazu Hassan @Katsina Times
Wani binciken da jaridun Katsina Times suka yi da hadin gwiwar wasu 'yan jaridun kasar Nijar, sun gano Attajirai da 'yan kasuwa 'yan asalin kasar Nijar mazauna Najeriya na taimakon kasar su ta Nijar sosai daga halin da kasar ta shiga sakamakon juyin mulkin da aka yi.
Binciken ya nuna akwai manyan attajirai masu kudin gaske da suka gina kasuwanci su a Najeriya, kuma suke zaune da iyalansu da 'yan'uwansu a Najeriya.
Binciken ya gano akwai wadanda aure ne ya hada su da 'yan asalin kasar Nijar, kuma auren ya haifar da zuriya masu karfin gaske.
Binciken ya gano akalla akwai sama da 'yan Nijar mazauna Najeriya miliyan 10 a cikin kasar nan suna gudanar da sana'o'i kala-kala, kuma mafi yawan su suna zaune lafiya da al'umma, kuma suna sana'o'insu na halal.
Binciken ya gano sama da 'yan Najeriya miliyan 20 ke da alakar auratayya ko dangantaka ta jini da 'yan Nijar.
A wata hira da shugaban mulkin soja na kasar Nijar ya yi, wadda aka watsa a duniya kwanan nan, ya tabbatar cewa 'yan Nijar mazauna Najeriya na kawo wa kasar tallafin daga halin da kasar ta shiga na takunkumi.
Bincikenmu ya gano attajiran Nijar mazauna Najeriya na taimakon kasar su ta hanyoyi danban-daban. Wadanda ke da kudin gaske suna daukar nauyin magana a kafofin watsa labarai don a jawo hankalin gwamnati kar ta dau wani mataki a kan kasar Nijar.
Wasu kuma daukar nauyin ganin mutane masu tasiri suke don su yi magana ga masu fada-a-ji a kasar a kan kasar su.
Kazalika, binciken namu ya gano suna daukar nauyin kafofin watsa labarai da sojan-baka, hatta 'yan Majalisar Tarayya ta Kasa wadannan attajirai sun shiga cikin su.
Wasu kuma taimakon da suke bai wa kasar su ita ce tattara ruwan kudi suna kai wa kasar domin a sanya a ayyukan raya kasa ko biyan albashi.
Wasu kuma danginsu suke taimako da abinci da kudin gudanar da rayuwa.
Binciken mu ya gano bisa tsari suke ayyukan su, kowa da abin da zai kawo karkashin wani attajiri dan asalin Yammai mazaunin Abuja.
Binciken ya nuna da yawan su suna goyon bayan soja masu mulki a Nijar saboda bambancin kabilanci da yankin da aka fito.
Nijar kasa ce wadda kabilanci ya yi mugun tasiri da katutu a cikinta. Tasirin kabilanci na hana ganin gaskiya ga mai mulki.
Bincike ya nuna da tsohon shugaban kasar Muhammad Bazoum daga wata babbar kabila ya fito da wannan juyin mulkin bai nasara ba.
Binciken ya gano goyon bayan da Janar Abdourahmane Tchiani (Omar Tchiani) ke samu na kabilanci ne ba zallar kishin kasa ba.
Wannan binciken an yi shi ne da hadin gwaiwar wasu 'yan jaridun kasar Nijar.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762
Email: newsthelinks@gmail.com
Email: katsinacitynews@gmail.com