Hukumar Hizbah Ta cigaba da rangadin Tattaunawa da Malaman Addini a Katsina
- Katsina City News
- 11 Feb, 2024
- 645
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar Hizbah ta jihar Katsina wato (Katsina State Hizbah Board) ta cigaba da rangadin da ta fara daga ranar Alhamis 7 ga watan Fabrairu na ziyartar Malaman Addinin Musulunci, Jami'an tsaro da masu rike da sarautun gargajiya a birnin Katsina.
Ziyarar na da nufin, Neman hadin kai, Addu'a amsar shawarwari da goyon baya bisa ayyukan sabuwar hukumar ta Hizbah da Gwamnatin jihar Katsina ta kafa, da nufin kawo gyara a cikin al'umma.
Dakta Aminu Usman da akafi sani da (Abu Ammar) shine babban Kwamandan Hizbah na jihar Katsina, kuma bisa jagorancin sa tare da kungiyoyin Addini na ko wane bangare ne suke rangadin tare da gabatar da kai ga a Wajen malaman da aka je neman shawarar a wajensu.
Ziyarar ta ranar Asabar tacigaba da ziyarar Dattijo kuma Masani Sheikh Muhammad Namadi a Zawiyyar sa dake Unwalar Jangefe, Shugaban Kadiriyya na jihar Katsina Sheikh Ahamed Rufa'i Kofar 'Yandaka, Sheikh Habibu Yahya Kaura, Sheikh Yakunu Musa Hassan Sauti Sunnah, Babban Dankasuwa Alh. Ladan Wapa, Sheikh Khalifa Dayyib Sani Zanguna da Dakta Aminu Yammawa.
Ziyarar bisa rakiyar Shugaban gudanarwa na hukumar, da shugaban sashin kudi na hukumar Hizbah da Yan jarida tare da sauran 'yan rakiyar ta bada armashi inda ko wane malami aka ziyarta yake nuna farinci da fatan alheri gami da nuna goyan baya dari bisa dari.
Ana saran hukumar zata yi irin wannan rangadin a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar Katsina don ganawa da malamai da jami'an tsaro.