An ɗaukewa Karamar Hukumar Jibiya Biyan Kuɗin Wutar Lantarki (NEPA)
- Katsina City News
- 02 Feb, 2024
- 483
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Shugaban Karamar hukumar Jibiya Hon. Bishir Sabi'u Maitan ne ya sanar tare da miƙa Cakin kudi (Check) na Naira Miliyan biyu (2,000,000) ga Ma'ajin hukumar samar da wutar lantarki na jihar Katsina a yammacin ranar juma'a.
Hon. Maitan yasha Alwashin cigaba da biyan kudin Nepa, na wata-wata na ƙaramar hukumar Jibiya ga Kamfanin samar da wutar lantarki na jihar Katsina har iya wa'adin Mulkinsa a karamar hukumar.
Yace "Mun dauki wannan matakin ne domin rage radadin wahalar rayuwa da ake fama da shi wanda wani ma a watan bashi da ikon da zai biya kudin wutar lantarkin"
Ma'ajin kudi na Kamfanin Kedco ya amshi Cakin kudin a madadin Manajan Kamfanin reshin jihar Katsina, inda ya bayyana jin dadin sa akan wannan yunkuri da shugaban karamar hukumar yayi, yace wannan ya kawo sauki hatta ga ma'aikatan su ga baki daya.
Shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Jibiya Alhaji Surajo Ado ya bayyana jin dadin sa da kuma jan hankali ga Kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Katsina da cewa "kamar yanda aka same su har ofishin su aka sauke nauyi a hukumance" yace "Don Allah kada ku bamu kunya mu 'Yan Siyasa ne, idan wuta ta samu a bama karamar hukumar Jibiya, idan bata samu ba mun san cewa ba laifin ku bane, kada ku hana mu wuta saboda wani dalili idan kukai haka ba ku za'a zaga ba mu za a zaga, ace Shugaban karamar hukuma ya yaudari mutanen sa, don haka kun ja mana zagi ga al'umma. Ya bayyana.
A karshe yayi fatan Alheri da kuma neman Addu'o ga al'ummar ta karamar hukumar Jibiya akan samun cikakken zaman lafiya.
Shugaban karamar hukumar Hon. Bishir Sabi'u Maitan ya samu rakiyar Mataimakin, Sakataren Karamar hukumar, Shugaban Jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar ta Jibiya.