Asalin Sarautar Tafidan Katsina
- Katsina City News
- 30 Dec, 2023
- 988
Tun farkon kafuwar mulkin Habe/ Korau (1348) akwai tsarin Sarautu na Gargajiya Wanda Muhammadu Korau da sauran Sarakunan Habe suka shinfida. A lokacin da Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina wajen shekarar 1806, Sai yaci gaba da tafiyar da wannan tsarin na Sarautu, amma akan tsarin Shariar Musulunci ba Gargajiya ba. Tun daga wannan lokacinne a Daular Sokoto aka ci gaba da kirkirarar sabbin Sarautu, kamar Waziri, Sai da sauransu.
. Sarautar Tafida a Katsina tana daya daga cikin Sarautun da aka kirkira a lokacin mulkin Dallazawa. Mutum na farko da aka fara nadawa wannan Sarautar shine Tafida Dodo Dan Sarkin Katsina Ibrahim (1869-1882).
A lokacin mulkin Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ya nada Alhaji Musa Yar'adua a matsayin Tafidan Katsina. An haifi Alhaji Musa Yaraadu a shekarar 1912. Yayi Karatu a Katsina College daga shekarar 1925-1930. Yayi aiki da maaikatar NA ta Katsina daga shekarar 1953-1959. Acikin Shekarar 1959 ya zama Ministan Lagos har zuwa shekarar 1966.
A lokacin mulkin Sarkin Katsina Alhaji Muhammad Kabir Usman (1981-2008) aka canza ma Alhaji Musa Yar'adua Sarautar Tafida zuwa Sarautar Mutawalle Katsina, wadda Mahaifin shin Mutawalle Ummaru ya taba yi a lokacin Sarki Dikko. Sai Kuma aka nada dansa watau General Shehu Musa Yar'adua a matsayin Tafidan Katsina. An haifi Shehu Musa Yar'adua a shekarar 1943. Bayan ya Kare karatunshi na Primary a Katsina, Sai ya wuce zuwa Katsina provincial Secondary School a inda ya kareta a shekarar 1962. Daga nan ya wuce Makarantar Sojoji ta Kaduna. Yayi Kwasa kwasai da dama akan aikin Soja anan Nigeria da Kashen waje. Wanda daga karshe har ya rike mukamin mataimakin shugaban Kasar Nigeria.
A halin yanzu Alhaji Murtala Shehu Musa Yar'adua shine Tafidan Katsina.
Musa Gambo Kofar soro