YADDA TURAWAN MULKIN MALLAKA SUKA MAMAYE DAULAR USMANIYYA.
- Katsina City News
- 20 Dec, 2023
- 753
Daular Sokoto ko Kuma Daular Usmaniyya ta samo asalintane a sanadiyyar Jihadin Shehu Usman Danfodio a cikin shekarar (1804). Mujaddadi Shehu Usman Danfodio shine Jagora na wannan Jihadi da aka gudanar a Kasar Hausa dama wasu makwabtanta. Wanda asabili da Jihadinne aka kafa Daular Sokoto ko Kuma Daular Usman, data kunshi garuruwa kamar Sokoto, Kano, Katsina, Zazzau, Hadejia, Gombe, Bauchi, Gwandu, Daura, Adamawa, Nufe, Katagum, Kazaure, Misau, Ilorin da sauransu.
Wannan Daula ta Sokoto ta rayu har tsawon Shekara dari da wani Abu. A cikin shekarar 1900 ne Turawan Mulkin Mallaka suka shigo Daular Sokoto da niyyar su MAMAYE ta ko Kuma su cita da yaki. Kamin Turawa su shigo Daular sun fara aikama Sarkin Musulmi Attahiru I wasika cewa ko yabi umarnin su ko Kuma ya fuskanci Yaki. Wannan ya jawo taron Sarakuna na Daular Alan yadda Zasu fuskanci Turawan Ingila na mulkin Mallaka, wasu sun bada Shawarar 1. A Yakesu. 2. Wasu Kuma sun bada Shawarar ayi zaman lafiya dasu, ayi masu Abinda suke so. 3. Wasu Kuma cewa sukayi ayi gudun Hijra.
Daga karshe Sarkin Musulmi Attahiru ya yanke Shawarar fada da Turawa, a inda suka gwabza Yaki a Filin Giginya cikin Sokoto, Wanda yayi sanadiyyar shahadar Mutanen Daular dadama. Bayan da Turawa suka ci Sokoto, cibiyar Daular Sai Kuma suka bi sauran Kasashen Daular da niyyar Yaki. A Kano an gwabza Yaki Tsakanin Yan mulkin Mallaka da da Mutanen Kano, a karkashin Jagorancin Sarkin Kano Aliyu Babba. Bayan Turawa sunci Kano, sunci Sokoto, da Hadejia da sauransu, Sai suka karkata akalarsu zuwa Katsina. Lugard ya rubutama Sarkin Katsina Abubakar wasikar cewa ga Turawan Mulkin mallakanan zuwa Katsina, ko suyi mubayaaa a garesu ko Kuma a Yakesu. Daga karshe Sarkin Katsina Abubakar ya yanke Shawarar biyayya ga Turawa ba tare da Yaki ba, haka Kuma akayi a ranar 28- ga watan Maris a shekarar 1903 Turawan mulkin Mallaka suka shigo Katsina ta Kofar Yandaka, aka tarbesu aka sabkar dasu Gidan Yarika ba tareda fada ko Yaki ba. Katsina shine Gari na karshe Wanda suka Mika wuya ga hannun Turawan Mulkin Mallaka a Daular Usmaniyya.
Shi Kuma Sarkin Musulmi Attahiru I, ganin cewa Turawa sun MAMAYE gaba dayan Daular Sai yayi Kira ga Sarakuna cewa su gudu domin gudun Hijra zuwa Saudiyya, a cikin shekarar 1903. Wannan ya jawo jamaa da dama daga cikin Daular suka ansa Kiran Sarkin Musulmi , suka dosa tafiya har Saida suka Isa wani kauye Mai suna Burmi, Wanda a halin yanzu Yana cikin Kasar Gombe, anan Turawan Mulkin Mallaka suka tarbesu sukayi masu zobe, nan take aka sake gwabza wani yakin, watau yakin Burmi, Wanda yayi sanadiyyar shahadar kusan mutum 200 harda shi Sarkin Musulmi Attahiru I, Wanda har yanzu kaburburansu suna can a Garin Burmi.
Bayan wannan nasara ta Burni da Turawa suka samu Sai Kuma suka bi duk wani Wanda suke tunanin zai kawo masu makalkashi ga Mulki suka Kama shi suka tsare. Mafi yawan Sarakunan da Turawan Mulkin Mallaka suka cire daga Sarauta sun kaisu Garin Lokoja a matsayin Yan gudun Hijra.
Daga cikin Sarakunan Daular Usmaniyya da Turawa suka Kai Lokoja akwai.
1. Malam Muhammad Lawal Kwasau. Sarkin Zaria. An kaishi Lokoja a cikin shekarar 1904, ya rasu a Lokoja acikn shekarar 1918.
2. Sarkin Kano Aliyu Babba. An kaishi Lokoja 1906, ya rasu a Lokoja 1926
3. Sarkin Konragora Ibrahim Nagwamatse. An kaishi Lokoja 1902 , ya bar Lokoja 1903.
4. Sarkin Zaria Aliyu Dansidi. An kaishi Lokoja 1922, ya rasu a Lokoja 1926.
5. Sarkin Abuja Ibrahim. An kaishi Lokoja 1902 ya rasu a Lokoja Acikin shekarar 1902.
6. Sarkin Katsina Malam Yero an kaishi Lokoja 1906 ya rasu a Lokoja 1919. Da sauransu.
Ta hakane Turawan Mulkin Mallaka na Ingila suka bi suka murkushe duk wani yunkuri daka iya kawo masu cikas ga mulkinsu.
Musa Gambo Kofar soro.