TARIHIN UNGUWAR ADORO
- Katsina City News
- 10 Dec, 2023
- 687
TARIHIN UNGUWAR ADORO
Unguwar Adoro tana daga cikin unguwanni na Yayan Sarakunan Dallazawa da ake Kira Sansanin Yan Sarki. Unguwar Sansanin Yan Sarki ta fara tun daga bakin Masallacin Juma'a zuwa Unguwar Madawaki, Gidan Waya, Unguwar Alkali, Sararin Kuka, Unguwar Yari, Unguwar Yarima, da ita kanta Adoron.
Unguwar Adoron ita dai ta samu wannan sunane ta dalilin wata Tsohuwar itaciyar Cediya wadda ake kyautata zaton cewa duk wani gida dake nan ta girme shi, shi kansa babban gida da ake Kira Gidan Bebeji anan ya sameta.
Ita wannan itaciya tayi wani doro ta lankwasa Kasa, wannan shine asalin dalilin da wasu mutane ke cewa itaciya Mai doro, yau da gobe aka takaita Kiran ana cewa Adoro.
A karkashin wannan itaciyane Bebeji Yusuf Abubakar da sauran yan'uwansa suke zama suna hutawa, idan Yamma tayi, har zuwa lokacin rasuwarsa.
Hakanan Kuma akwai wata mashahuriyar Rijiya da ake kyautata zaton an gina ta lokacin da aka Gina babban gida dake nan Adoro. Tarihin wannan ya nuna tunda aka ginata bata taba kafewa ba, Kuma ana zuwa daga unguwanni daban daban na Birnin Katsina ana dibar ruwanta. Amma yanzu babu wannan rijiyar, kasancewar Titi ya ratsa ta inda take a lokacin Gwamna Ummaru Musa Yaradua.
Koda yake tun kafin a gina babban gida na Adoro, Wanda ake Kira Gidan Bebeji Yusuf Abubakar, akwai wasu manyan gidajen Dallazawa a Unguwar Adoro da suka hada da
1. Gidan Machika Abdu Doro
2. Gidan Abdulmumini Lambisa
3 Gidan Dan Yusufa Yahaya
4. Gidan Alu
Wadanda dukkansu yayan Sarkin Katsina Ibrahim ne. Gidan da Gatari Mamman yake nan ne asalin Gidan Sarkin Katsina Abubakar, kafin ya zama Yarima har daga baya ya zama Sarkin Katsina duk a wannan Gidan yake.
ABUBUWAN TARIHI NA UNGUWAR ADORO SUNE.
1. Itaciya Mai Doro
2. Rijiyar Adoro
3 Kabarin Bebeji Tukur
4. Kabarin Gatari Mamman
5 Kabarin Matar Sarkin Katsina Ibrahim, diyar Sarkin Musulmi Abubakar Mai Raba, watau ( Khadijatul Kubura).
MASHAHURAN MUTANEN DA SUKA FITO DAGA UNGUWAR ADORO
1. Alh. Armayau mahaifin Dr. Yushau Armayau
2. Alh. Mamman Anade
3. Alh Ummaru Lafiya Uwar Jiki
4. Alh Kabir Yusuf ( Maaikacin Jaridar DailyTrust).
5. Fatima Abbas Hassan ( NTA).
TA FANNIN MALAMAN ADDININ MUSULUNCI
1. Akwai Professor Abdulrahman Lawal Adoro. Mai waazi a gidajen Radion Vision FM da Alfijir da sauransu
2. Akwai Gidan Malam Yahaya, mahaifin Malam Yakubu Yahaya, shugaban Yan Shi'a na Katsina.
.TA FANNIN MAKADA.
1. Akwai Sarkin Taushin Katsina
2. Sarkin Tuta
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.