Kwamandojin Kungiyar Hamas. SH. YAHYA AS- SINWAR, SHUGABAN KASAR GAZZAH. Daga shiek Aminu Aliyu Gusau
- Katsina City News
- 08 Dec, 2023
- 653
A shekarar 2011 gwamnatin Isra'ila ta shiga yarjejeniya da Hamas, tana son Hamas ta sakar mata wani soja daya tilo da take tsare da shi kusan shekara biyar. Sunan sojan Gilad Shalit. Isra'ila ta yarda ta saki fursunoni 1,026 na Falasdinawa akan wannan sojan daya .
Daga cikin wadannan mutane 1,026 da aka saki akwai Yahya Sinwar, wanda a lokacin ya shafe shekaru ashirin daidai gidan yari inda ya ke dauke da daurin rai da rai sau hudu. A lokacin da yake gidan yarin ya taba samun cutar wani tsiro a cikin kwakwalwarshi (Brain tumor) wanda zai iya hallaka shi amma ma'aikatan kurkuku suka kai shi asibiti aka yi mashi tiyata ya samu lafiya.
A yau babu abunda yahudawa suke nadama kamar sakin Yahya Sinwar basu barshi ya mutu can ba, da kai shi asibiti basu barshi ya mutu da cutarshi ba. Domin kuwa yanzu Yahya Sinwar shine shugaban kasar Gazzah karkashin jam'iyyar siyasa ta Hamas, kuma shine babban jigo wanda ya ke zaune daram a cikin Gazzah daga cikin masu hannu a cikin shiryawa da jagoranta da aiwatar da abubuwan da suka faru ranar 7/10/23.
Gashi kuma tun shekaru da dama sun yi ta kokarin kashe shi amma basu samu nasarar ba. Misali a watan biyar na 2021 yahudawa sun jefa bama-bamai a gidanshi domin su kashe shi. Kwana biyu bayan haka sai ya bayyana a wani taro ya ba da sanarwa cewar yanzu nan zai yi zagayen titunan Gazzah da kafa na awa daya. Idan yahudawa suna son su kashe shi to su yi amfani da wannan awa dayar, in ba haka ba kuma to sun makara. Haka ya yi zagayenshi a kasa na awa daya ya sake bacewa.
Yanzu hakan nan a wannan ruwan bama-bamai da yahudawa suka yiwa Gazzah babu wanda suka fi so su kashe kamar shi amma kwanan shi bai kare ba.
Zamu kawo maku takaitaccen tarihin Sh. Yahya As-Sinwar in sha Allah.
Modibbon Gusau.
29/11/23.
Mun Ciro daga shafin Attajid Media