TARIHIN MARIGAYI SHEIKH MUNTAKA COOMASSIE
- Katsina City News
- 30 Nov, 2023
- 899
Ina fatan Mutane da yawa dake neman Tarihin Marigayin musamman Daliban Jami'oi na Nigeria da K'asashen Waje dake rubutun Project da wad'an da suke son rubutawa akan shi har dama wad'an da suka riga suka rubuta, zasu k'ara amfana da wad'an nan bayanan.,
BISMILLAH!!!
Cikakken sunan Sheikh dai, shine "Muhammad Muntaka Ibn Muhammad Sani Ibn Ya'Kub al- Kusadiyyil al- Kashnawi*.
Shi jika ne wurin Imam Ya'Kub Ibn Bawa Ibn Kusadiyyil al-Kashnawi.
Ainahin tushen zuri'an Bani Coomassie, sun fito daga garin Kusada ne ta Jihar Katsina.
An haifi Sheikh Muntaka Coomassie ne a wani gari da ake kira Kintampo, kusa da Kumasi ta kasar Ghana, wajen shekaran 1916. Mahaifin sa Malam, Muhammad Sani Ibn Yakubu Kusada, k'ani ne ga Malam Sallau, Sarkin Zangon Kumasi. Ciki d'aya suka fito. Bayan rasuwan Malam Sani, mahaifin Sheikh Muntaka a lokacin yana dan k'arami kwarai, sai ya koma k'ark'ashin kulawan kawun nasa, Sarki Malam Sallau. Shiekh, ya taso tare da Yayan shi watau D'an Malam Sallau, mai suna Malam Ahmadu Coomassie.
Sheikh Muntaka ya shiga Makarantar allo na Malam Sallau, wacce ta Addini ce da kawun nasa ya assasa. Daga nan kuma sai ya shiga Makarantan Primary. Sheikh Muntaka, d'alibi ne mai matukar hazaka. Domin ya haddace AL QUR'ANI mai Tsarki yana d'an shekara goma sha daya (11) da haihuwa.
Sheikh Muntaka, ya kuma rubuta AL QUR'ANI mai Tsarki yana d'an shekara goma sha shida (16) a Duniya. Sheikh d'in, yafi maida hankali a fannin karatun Addini, duk da yake ya nemi ilimin zamani haik'an.
Bayan wani lokaci mai tsawo, Sheikh Muntaka da Kawun nasa Sarki Malam Sallau, suka dawo gida Katsina. Lokacin da Sheikh ya kai munzalin yin aure, an aura masa mata mai suna Fatima (Mami). Ita Mami, jika ce wurin Sarkin Zangon Kumasi. Mahaifiyar ta kuma, d'iyar Saratu ce, ita kuma Saratu, d'iyar Hauwau ce, uwargidan Sarki Sallau.
Lokacin da ÀLLAH YA tashi ba Sheikh rabo, YA bashi d'iya mace mai suna Tsayyaba, amma bata jima ba ta rasu. Haihuwa na biyu namiji ne amma shima ya rasu wurin haihuwan.
Sheikh Muntaka Coomassie, ya halarci makarantan Midil ta Katsina, a tsakiyar shekaran 1930. Yana daga cikin d'alibai masu hazak'a kwarai dagaske. Hakan yasa bayan kammala karatun, aka zab'e Shi da da marigayi Colonel Iliyasu Wali da marigayi Malam Ahmadu D'anbaiwa da kuma marigayi Alh Ladan Baki, aka basu gurbin zuwa karatun zama Injiniyoyi a Kasar Ingila. Koda yake Kafin nan, an tura Sheikh Muntaka aiki a b'angaren Injiniyoyi ta N.A anan Katsina.Da yake Sheikh yana da ra'ayin son zurfafa ilimin Addini , sai yasa k'afa ya shure wannan daman tafiyar. Yace shi yafi bukatar zama Malamin Addini. Da Sheikh yaga ana neman tilasta mishi, sai ya gudu ya bar garin..
Zangon sa na farko da yayi shine a wani gari mai suna Yendi. Anan ne ya auri matar sa ta biyu, mai suna Halimatu, wacce ita ce mahaifyar marigayi, mai shari'a a Kotun Koli, Just Saifullahi. Daga nan sai ya wuce zuwa garin Birnin Kebbi, a lokacin zamanin Sarkin Kebbi, marigayi Malam Yahaya. Anan ne Sheikh Muntaka ya sadu da Babban Malamin shi, marigayi Malam Kwasau. Ya yayi zaman sa na shekaru da yawa yayin da Katsina ana ta neman shi.
Kamar yanda ya saba, anan ma, bai zauna ba domin ya cigaba da shiga lunguna da k'auyuka, domin neman k'arin ilimi da yin bincike-bincike akan harkokin addini wuren masana..A nan Birnin Kebbi ne, Sheikh ya k'ara samun wani haihuwan na marigayi Malam Abdulhakami.
Tun lokacin da Sheikh Muntaka ya bar gida Katsina, an sami tsawon lokaci ba'a san inda yake ba duk da bincike da akayi tayi ta wajen Sarakuna daban daban. Bayan addu'oi da bincike mai tsanani da d'an uwansa(Yayan shi), marigayi Malam Ahmadu Coomassie ya yi, tare da gudunmuwar marigayi Malam Abubakar Imam, da margayi Walin Katsina Malam Bello Kagara, da kuma marigayi Malam Ahmed Metteden na Kano, a k'arshe dai suka gano wurin da Sheikh ya b'oye, watau anan Birin Kebbi.
Daga nan suka same shi tare da matsa mishi lambar sai ya dawo gida.
A cikin shekaran 1945 ne, Sheikh ya komo amma yace, Zaria ne zai zauna saboda garin ilimi ne. Isowar shi Zaria, sai ya sauka a wurin Alhaji Bawa dake Bakin Kasuwa. Daga nan ya koma Kwarbai, gidan Sarkin Shanu Danburan Dikko sai kuma Unguwar Liman daga nan ya koma Unguwar Juma gidan Alkali Kawu.
Anan Zaria ne ya auri matar shi ta uku, mai suna Hadizatu wanda ake kira da (Inna/Fuloti ). Ita d'iya ce ga marigayi Malam Ibrahim, d'an marigayi Ma'aji Yahaya dake Bakin Kasuwan Zaria. Jikanya ce kenan gashi marigayi Ma'aji Yahaya.
A k'arshe dai bayan ya kammala ginin gidan shi anan Unguwar Alkali, sai ya tare.
Abin tarihi da sha'awa, tarewan shi a gidan babu jimawa sai ALLAH YA bashi haihuwan Alhaji Ahmad, wanda yayi Babban Jami'in Hukumar Aikin Hajji ta K'asa (NAHCON) mai kula da shiyar Kaduna na tsawon shekaru 25 a wannan kujeran. Tun lokacin Jihohi kamar 7 suke k'ark'ashin shi. Alh. Ahmad Coomassie, shine wanda Sheikh ya fara haihuwa anan gidan nashi na Anguwar Alkali, a shekaran 1956.
Shi Sheikh, mutun ne mai bibiyan Malamai musamman indai yasan zai k'aru da kuma shima ya bada gudunuwa gare su. Don haka a Zaria ma haka ya yi k'ok'arin saduwa da mashahuran manyan malai irin su: Malam Musa na Magajiya, Wazirin Zazzau Malam Lawal, Alkalin Zazzau Malam Yahuza , Ma'aji Malam Isyaku, Malam Abdurrahman Kofar Doka, Malam shuaibu Yabo, Limamin Kona ., Malam Na'iya da wasunsu da dama..
Bayan zuwa neman ilimi da yake yi shima bai fasa karantarwa ba ga irin wadannan mutane a fannonin da ÀLLAH YA bashi fahimta., Sheikh Muntaka mutun ne mai zurfafa bincike akan harkokin Addinin Musulunci, Kuma yayi rubuce rubucen littafai da dama lokacin rayuwar shi.
Sheikh, mutum ne mai sana'oi. Bai yarda da rashin abinyi ba. Shi babban manomi ne da ya mallaki gona makeke a k'auyen Dumbi. A lokacin, har marigayi Sardaunan Sokoto kan biya ta gonar akan hanyar shi na wucewa.Yana cikin sahun mutane na farko da suka fara noman zamani a Arewacin Najeriya, musamman na Auduga. Har Itace, Sheikh ya saiyar.
Haka kuma yayi kiwon kaji sosai. Shi yake baiwa ABU Kongo (Catering ) kwai da Kaji. Har da Malamai, Turawa dake ABU Samaru.
Sheikh ta kai har ya sayi k'aramar Motan shiga ( Renault R4) da Kud'in kwai da kaji a shekaran 1966/1967.
Sana'ar sufuri ma haka. Yayi motocin haya lokacin marigayi Alh Bature Kwangero, shine shugaban Dirobobin.
Sheikh Muntaka, yayi aiki da Institute of Administration ABU_ Kongo a B'angaren Mulki da Sharia. Ya kasance Babban mai Koyar/Horar da Alkalan kotunan N.A. na Arewacin Najeriya a cikin shekarun 1953-1960. Bayan nan ne ya zama Babban Sufeto mai duba Alk'alai na Arewa.
Sheikh na cikin Komitin Muffet da marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya nad'a akan binciken Mai martaba Sarkin Kano Sanusi.
Bayan juyin mulkin shekarar 1960 ne aka maida shi kaduna, Ma'aikatar Shari'a. Daga bisani kuma zuwa Ma'aikatan ilimi.
Bayan an k'irk'iro Jihohi goma sha biyu (12), sai akayi mishi canjin wuri, zuwa Jihar Katsina a matsayin Baban Sufeto na kotunan Area Katsina.
Isar shi Katsina, sai ya fara zama a gidan da d'anuwanshi marigayi Malam Ahmadu Coomassie ya tashi a Unguwar Yar'adua. Bayan Sheikh ya gama ginin nashi gidan dake Anguwar Kwad'o bisa hanyar Daura a shekaran 1969, sai ya tare.
Wajen shekaran 1970 zuwa farkon 1971, Sheikh ya koma Ma'aikatan Ilimi, a sashen Arabic. Daga nan ya bar aiki saboda hankalin shi na wajen neman K'arin ilimi, musam man a k'asashen Larabawa. Daga bisani ya yanke hukuncin yin Hijirah zuwa k'asar Saudi Arabia..
Gwamnatin Nigeria a lokacin marigayi Shehu Musa Y'aradua shine Chief of Staff, Supreme Military Headquarters, a Dodon Barracks, suka matsa ma Sheikh da su bashi Appointment don ya zama mai taimaka ma Offishin Jakadancin Nigeria, watau Nigerian Embassy, (Hajj Mission) bisa wasu abubuwan da ya shafi Addini da kuma maido da kiman Nigeria a k'asar, saboda zubar da mutuncin da wasu tsuraru suka yi tayi.
Hijirah:
A cikin watan November 1971 ne, Sheikh ya bar Nigeria zuwa k'asar Saudia Arabia inda ya zauna a garin Jeddah.
D'abian Sheikh duk inda yake son yin muhalli, yafi son nesa da gari. Yakan ce yafi samun natsuwa wajen maida hankali ga nazarorin da yake yi. Sakamakon hakan ne sau uku, Sheikh na canza muhalli a K'asar Saudia kasancewar duk in da ya zauna lokaci kad'an sai wajen ya zama alk'arya.
Sheikh saboda halakar shi da manyan Shaihunan K'asan Saudi Arabia yasa Sheikh Bin Bazz ya sanya shi cikin masu bada Fatwah anan cikin Makkah a Haram (1973) inda yake da D'aki a ciki, kamar yanda sauran masu bada Fatwah suke dashi.
Sheikh Muntaka Coomassie, ya jagoranci zaman sulhu tsakanin Manyan Malaman Nigeria da Gwamnatin Nigeria ta shirya tare da taimakon Admiral Sulaiman Saidu rtd. Anyi zaman ne lokacin aikin Hajji a filin Arafat akan batun banbancin fahimta game da Kablu da Sablu yayin sallah. A zaman, akwai ;
Sheikh Muntaka Coomassie (Shugaban zaman),
Sheikh Ibrahim Sale
Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh ABUBAKAR Gumi
Sheikh Nasiru Kabara.
Akwai shi kanshi Admiral S. Saidu da kuma Radio Tarayya na Kaduna wanda sukai ta aiko da muk'abilan kai tsaye.
Alhamdulillah a zaman, duk sun fahimci juna inda a k'arshe, Sheikh Muntaka ya bukaci da suyi suyi Sallolin Zuhur da Assar tare. Ya ba Sheikh ABUBAKAR Gumi damar yin Limancin Zuhur, shi kuma Sheikh Dahiru Bauchi yayi Limancin Assar. Kuma dukka sunbi.
Akwai takardan sanya hannun dukkan Malaman na amincewa da sakamakon zaman wanda marigayi Sarkin Musulmi Abubakar ya ummurta da suyi.
Sheikh Muntaka Coomassie, yayi tafiye tafiye K'asashen Duniya masu yawa domin fad'ad'a neman Ilimi da saduwa da manyan Malamai. Kad'an daga irin K'asashen da ya tafi sun had'a da:
Mali, Senegal, Morocco, Spain, Tunisia, Singapore, Egypt, Malasia, Libya, Iran, Iraq, Jordan, Syeria, Algeria, Paris, India, Indonesia, Mauritania, Ethiopia, Afghanistan, Pakistan, UAE da sauran su. Wasu tafiye tafiyen, Bankin Musulunci (Islamic Bank) dake da Headquarter a Jeddah suka d'auki nauyi.
Burin Sheikh abu biyu. Cikawa da imani da zamowa Kabarin shi yayi mak'otaka da Annabi (S A W) a Madinah. Alhamdulillah ya sami haka domin yana kan rubutun wani Littafin shine mai Volumes 8, a ranar wata Juma'ah dai Sallar Assar, ÀLLAH YA dauk'i ran shi. Yana rike da Littafin da yake aiki akai.
Wani ikon ÀLLAH kuma, a ranar kafin sallar Juma'ah, Alh Aminu Dantata wanda ya dauki Sheikh a matsayin Uba kuma a lokacin yafi zama a Saudia ya biyo gidan Sheikh akan hanyar shi na zuwa Sallar Juma'ah a Makkah. Sheikh.yaçe mishi, lallai yayi k'ok'ari ya tafi dashi garin Madinah a ranar. Alh yayi alkawarin In shaa ÀLLAH zasu tafi a Jirgin karfe 8:30 na daren,.
ÀLLAHU AKBAR! Dawo wan Alh Aminu Dantata daga Makkah ya sake biyo gidan, kawai sai gawan Sheikh ya iske..
Sheikh ya rasu anan gidan shi dake kan hanyar Jeddah zuwa Makkah. Gwamnatin K'asar Saudia ta umurci da akai gawan shi zuwa garin Madinah, inda tasa aka binne shi anan cikin Bahkeeyah.
Burin shi ya sake cika ta wajen amincewar mu Y'ay'an shi na sadaukar da dukkan littafan karatukan shi domin amfanin Al'umma. Dama can baya ya.rok'i Tsohon Shugaban Nigeria Gen Ibrahim Babangida da ya taimaka bayan ranshi yanda zai gina Library na Musulunci a Zaria wanda shi General Babangidan ya fara aikin kuma da taimakon tsohon Shugaban Yan Sanda Nigeria, Marigayi Ibrahim Ahmadu Coomassie yayi magana da Marigayi Shugaba General Sani Abacha aka kammala aikin, kuma aka sanya littafan. Marigayi Sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris ne ya bud'e.
Sheikh ya rasu ya bar Y'a'ya 33 a Duniya. Maza goma shad'aya (11), Mata ashirin da biyu (22), da Jikoki masu yawa.
A yanzu dai, Alhaji Ahmad Muntaka Coomassie, shine babba a cikin Y'ay'an nashi da suka rage.
Abin sha'awa kuma shine, daga cikin Y'ay'an da ya bari, guda goma sha biyu ne (13) ne kawai haihuwan Nigeria. Sauran duk haihuwan Saudia ne.. Kuma mafi yawan mata da mazan sunyi aure da Y'ay'a.
Littafan da Sheikh ya wallafa sun had'a da:
1. Tambayoyi da Amsoshi a kan Al'amurran Musulunci da Mutane ke Rikitarwa Vol 1 (1969)
2. Tambayoyi da Amsoshi a kan Al'amurran Musulunci da Mutane ke Rikitarwa Vol 2 (1982)
3. Fassarar Al- Ahdari Arabic da Hausa (1981).
4. Kabli da Ba'adi -Hausa (1975).
5. Littafin Mamaki (1954).
6. Tarjama Ma'ana Ihda Ashrata Suwar ila Lughati -Hausa (1983).
7. Ifsha'ul Salam min Wahhajah Arabi Vol 1-4 (1989).
8. Misbahul Zujajah fi Zawaid ibn Majah Vol 1-4 (1988)..
9. Khawakibul Wahajah Vol 1-4,
Saura Vol 5-6 da bai sami yiba.
Karin bayani, Sheikh har Kamfanin buga littafai ya bud'e acan Jeddah, Saudi Arabia mai suna "Takarda Islamic Publications Ltd". Mafi yawan littafan shi anan aka buga su. Wasu kuma a kasar Cairo, yayin da ni kuma nake shigowa dasu nan Nigeria domin raba ma masu ciniki damu a garuruwa daban daban a matsayi na Manager Kamfanin.
ÀLLAH YA jikan Iyayen mu da Malaman mu gaba d'aya, YA had'a mu dasu a Aljannah. Alhamdulillah!!!
Ahmad Muntaka Coomassie.
(1st December, 2023).
SANARWA:
Na sadaukar da wannan bayanan ga d'inbin masu neman Tarihin shi da d'aliban Jami'oi daban daban na Nigeria da K'asashen waje, masu sha'awan rubuta Project game dashi har da masu kan rubutawan. ÀLLAH YA bamu sa'a gaba d'aya da saka muku da alkhari. Mungode.