JAMI 'AN "COMMUNITY WATCH" SUN FAFATA DA ƳAN BINDIGA . ...sun kashe wasu .wasu sun sha da kyar
- Katsina City News
- 26 Nov, 2023
- 994
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times
Jami'an tsaron "community watch corps"sun fafata da ƴan bindiga a yankin Batsari ta jihar Katsina.
Da misalin ƙarfe 9:30pm na daren asabar 25/11/2023. ƴan bindiga masu tarin yawa suka kaima jami'an tsaron community watch corps dake aikin bada tsaro a ƙauyen Watangaɗiya hari.
Yan bindigar Sunyi ƙoƙarin yima jami'an tsaron ƙawanya amma jami an da hadin gwiwar mutane garin suka dake akayi ta ɗauki ba daɗi, inda ƴan bindigai suka dinga antaya masu harsasi da bindigar girke ,wasu kuma da AK-47,kamar yadda wani mutumin garin ya tabbatar da jaridun Katsina Times.
Yan ta addar sun fi yan community watch manyan makamai da yawa amma duk da haka suka dage aka ɗauki lokaci ana fafatawa
Da barayin suka lura ba sa a, sai suka janye ,jikin su tare da daukar gawarwakin yan uwansu da aka kashe.
Da ƙura ta nutsa, jami'in tsaro ɗaya ya samu rauni, sannan sun sace babura huɗu, su kuma ɓarayin sun bugo wayar da suka sace sunce an kashe masu mutum uku.
Katsina Times
@www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
Www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762