Ana Zargin Jami'an Tsaron Community Watch da cin Zarafin magaji Batsari da Sule Abdullahi.
- Katsina City News
- 20 Nov, 2023
- 893
Daga Misbahu Ahmad Batsari @ Katsina Times
Jami'an Tsaron Community Watch sun Kai ziyara gidan Magaji Batsari, inda suka yi mashi kwasan Karan mahaukaciya suka wurga shi mota suka tafi da shi suka garƙame a ofishin su.
Lamarin ya faru a ranar lahadi 19-11-2023 da rana tsaka. A tattaunawar shi da wakilin mu bayan an sako shi, watau Magaji Batsari, Bishir Ado Batsari ya bayyana cewa tunda Allah ya halicce ni ban taɓa haɗuwa da cin zarafi da cin mutuncin da suka yi masa ba. Ya ƙara da cewa; "Na dawo daga Kano wajen jinyar ɗan'uwa na Lawal Rabe da akayi masa aiki a asibitin Kano, kawai sai naji anyi mani sallama nace masu wake sallama sukace jami'an tsaron ne na community watch, na fito na tambaye su mike faruwa sukace ance mu tafi da Kai, sai nace kuyi haƙuri inyi sallah inci abinci sai in iske ku ofis, sai naga ɗaya daga cikin su ya ware yayi waya, yana gama wayar sai yace su kama ni, take suka cakwakumeni kamar sun kama ɓarawo suka wurga mota a gaban iyalaina da mahaifiyata suka fizgi mota suna yi mani izgilanci suna cewa sai mu tattakaka, kai har ka isa ka riƙa gardama da mu. Suna isa dani sai suka jefani sal ɗinsu suka garƙame.
Ni kuma a ciki nayi taimama nayi sallar azahar, dana kammala sai suka miƙo mani takarda, da na duba sai naga takardar dakatarwa ce daga fadar mai martaba sarkin Ruma.
Bayan sun sallame ni na tafi gida mutane suka tarbe ni suna yi mani jaje wani daga cikinsu yake bayyana mani cewa wai ankama wasu shanu ne zaa kai kasuwa da takardar sheda daga Magaji Batsari".
Binciken mu ya tabbatar mana cewa wakilin shi ya bada takardar kuma an tabbatar da cewa shanun tsabtatattu ne.
Mun samu labarin wasu masu fada aji sun shiga maganar.har an janye takardar dakatarwar da aka aika masa.
A wani labarin kuma jami'an na community watch sunkai samame gidan wani mai suna Sule Abdullahi dake zaune a unguwar turaku Batsari, inda suka iske shi ƙofar gida yana hira da abokan arzikin shi, sai kwamandan su mai suna Sule Mamman yace ma yaran nashi su kama shi, nan take suka cafke shi suka falle shi ya faɗi ƙasa, sannan suka kwashe shi suka jefa mota suna duka suna zagi, mata da yaranshi suka fito suna kuka, mutane suka rugo suna tambayar dalili, sai suka bayyana masu cewa, anyi ƙarar shi wurin su ana bin shi bashi, wani mai suna Abdu Lawal ne yayi ƙarar shi, in kuma akwai wanda zai biya masa to ya biya.
Nan da nan mutane suka taru suna Allah wadai da wannan cin mutuncin da sukayi masa. Ganin mutane sunyi masu yawa kuma sun basu rashin gaskiya yasa suka sake shi.
Jaridun Katsina Times sunyi kokarin jin ta bakin Manyan jami an community watch amma duk Wanda suka tuntuba a waya sai yace baya da alhakin Magana.
Munyi kokarin magana da kwamishan tsaron cikin gida wayar shi bata shiga.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762