AN FAFATA DA BARAYIN DAJI, AN KAMA MUTUM BIYU.
- Katsina City News
- 20 Nov, 2023
- 823
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times
Mutane a ƙauyen Watangaɗiya dake karamar hukumar Batsari, sunyi artabu da ɓarayin daji har sun kama biyu a cikinsu.
Da safiyar yau litanin 20-11-2023 wasu da ake zargin ɓarayin daji ne su uku akan babur suka biyo wani da ya kuɓuce masu daga inda suke tsare da shi, wanda yana ɗaya daga cikin mutane huɗu da sukayi garkuwa da su ranar juma'ar da ta gabata a ƙauyen na Watangaɗiya dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Da shigowa garin mutane sukayi ta maza suka tunkare su inda sukayi masu ƙofar raggo suka cafke biyu daga cikinsu ɗaya kuma yasha da ƙyar. Ya zuwa yanzu har an hannunta su ga jami an tsaro ,domin cigaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Ganau sun ce Mutanen garin sun sha alwashin kare garin su har sai an fi karfin su.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762