Ziyarar Bangirma: Kungiyar Kanikawa (Nata) ta ziyarci tsohon shugaban Najeriya
- Katsina City News
- 16 Nov, 2023
- 708
Daga Muhammad Kabir, Katsina
Ƙungiyar kanikawa reshen jihar Katsina "Nigerian Automobile Technician Association" ta kaima tsohun shugaban ƙasar Najeriya Malam Muhammadu Buhari ziyarar bangirma a gidan sa dake a karamar hukumar Daura a jihar.
NATA ta kai ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar na jiha injiniya Abbati Muhammad, a Yau Alhamis 16/11/2023.
Da yake jawabi yayin ziyarar shugaban na NATA yace ziyarar nada nufin taya tsohon shugaban ƙasar murna na yadda ya fara mulki lafiya ya gama lafiya.
Ya kara da cewa "Wannan kungiya tana godiya bisa naɗa Engr Zailani Aliyu, a hukumar bunƙasa ƙera motoci ta Nijeriya "National Automotive Design And Development Council" karkashin ofishin sa ya horas da manbobin kungiyar sama da dubu".
Injiniya Abbati ya gode ma tsohun shugaban ƙasar ta yadda aka samar da wajen koyar da gyaran motoci na zamani a jihar.
Anasa jawabin yayin ziyarar, tsohon shugaban ƙasar ya bayyana jin dadinsa da ziyarar ta NATA, inda yace tsarin da kungiyar ke dashi abune mai kyau, na ganin yadda suka rage ma gwamnati aiki.