TA'AZIYYA DAGA FADAR GWAMNATIN KASA
- Sulaiman Umar
- 09 Nov, 2023
- 685
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin, yana da shekaru 73 a duniya.
Shugaban ya aike da sakon alhini zuwa ga iyalai, dalibai, da kuma mabiya wannan malami da ke Kano, da ma Masarautar Gaya wanda wannan malami ke kan karagar sarkin malamanta a lokacin rayuwarsa.
Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karade muryoyin jama'a a fadin kasar nan, duba da irin dimbin mabiyan da marigayin ke da shi musamman ma mabiyan darikar Tijjaniyya a ciki da wajen Najeriya .
"A matsayinsa na mai koyarwa, sha'iri, masanin shari'ar musulunci da tsirrai, kuma uwa uba malamin addinin Islama, Sheikh Yusuf Ali ya yi tasiri ga dimbin jama'a a tsawon rayuwarsa wadda ya sadaukar da ita kacokan wajen neman ilimi da yada shi" in ji shugaban.
Shugaba Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin da kuma gwamnatin jahar Kano da al’ummar jihar da ma daukacin Musulmin Najeriya bisa wannan rashi da aka yi ya na mai addu'ar Allah ya jikan Malamin.
Sa hannun mai bai wa shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin yada labarai,
Chief Ajuri Ngelale
Nuwamba 6, 2023