Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kaddamar Da Kasafin Kudi Naira Tiriliyan 2.17 A Cikin Sa'o'i 48 Domin Magance Matsaloli Sakamakon Cire Tallafin Man Fetur
- Katsina City News
- 04 Nov, 2023
- 774
A Yau Asabar ne Majalisar Dattijai ta Amince da ƙarin kasafin kudi na naira tiriliyan 2.17 a cikin sa’o’i 48, Saboda buƙatar magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.
A Cewar Mataimakin Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, Yin Gaggawar zartar da Kasafin aiki ne na kishin ƙasa.
Sen Ali Ndume ya bayyana cewa kasafin ya haɗa da tanade-tanade na Biyan mafi ƙarancin Albashi na N35,000 ga ma’aikata da lamuni Ga ɗaliban dake manyan makarantun Gaba da sakandare, Waɗanda aka amince dasu a yayin tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da Gwamnatin tarayya.
Ƙarin kasafin ya kuma ƙunshi tanadin wasu muhimman ayyuka, kamar abinci da sufuri, waɗanda suka yi tsada tun Bayan cire Tallafin mai.
Ndume yace majalisar Dattawa ta fahimci irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a lokacin da suke zartar da kasafin kudin, ya kuma bukaci Gwamnatin tarayya da ta aiwatar dashi cikin Gaggawa da kuma inganci.
KBC Hausa News