Daga Mu’azu Hassan
@ Katsina Times / Katsina City News
A shekarar 1966, gwamnatin Arewacin Najeriya ta wancan lokacin ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashir, domin gudanar da bincike kan wasu kadarori da aka danganta da shi.
A lokacin, Hukumar Kula da Kamfanoni da Kadarori ta Jihar Arewa ta yi zargin cewa ta gano wasu kadarori da ke da alaƙa da Sarkin, waɗanda ake zargin an mallake su ta hanyar da ba ta dace da doka ba.
Jaridar New Nigeria ta wancan lokacin ta wallafa wannan labari a ranar 16 ga watan Nuwamba, 1966, inda ta bayyana cewa an dakatar da Sarkin, tare da fara gudanar da bincike a kansa.
Bayan kammala binciken, Sarkin ya koma kan kujerar sarautarsa ta Daura, inda ya ci gaba da mulki har zuwa rasuwarsa a shekarar 2010, yana kan karagar sarautar Sarkin Daura.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page@,katsina city news
Facebook group. @Katsina city News
Facebook page @ jaridar Taskar labarai
You tube channel@ katsina times
Contact. 07043777779.


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!