Amuchie Ya Bukaci Kafofin Yaɗa Labarai Su Mayar da Hankali Kan Samar da Ilimi

Ya ce hakan zai taimaka musu wajen tsira a zamanin da ake samun labarai ba tare da ziyartar shafukan yanar gizo baKatsina TimesDr Maxwell Amuchie, mawallafi kuma Babban Darakta na…

Katsina City News October 10, 2026  ·  12:00 AM
| 84 Views
Amuchie Ya Bukaci Kafofin Yaɗa Labarai Su Mayar da Hankali Kan Samar da Ilimi
Amuchie Ya Bukaci Kafofin Yaɗa Labarai Su Mayar da Hankali Kan Samar da Ilimi



Ya ce hakan zai taimaka musu wajen tsira a zamanin da ake samun labarai ba tare da ziyartar shafukan yanar gizo ba


Katsina Times


Dr Maxwell Amuchie, mawallafi kuma Babban Darakta na kamfanin Sundiata Post Media Ltd, ya bukaci kafofin watsa labarai, musamman na Afirka, su sauya daga mayar da hankali kan samar da labarai kawai zuwa samar da ingantaccen ilimi da bincike domin tsira daga kalubalen zamani.


Amuchie ya bayyana hakan ne a yayin horon da aka gudanar a ranar farko ta taron shekara-shekara na Kungiyar Mawallafa Kafofin Sadarwa na Yanar Gizo ta Najeriya (GOCOP), a otal din Radisson Blu da ke Ikeja, jihar Legas.


Ya ce kafofin watsa labarai na gargajiya za su ci gaba da kasancewa masu muhimmanci, amma wajibi ne su rungumi sauye-sauyen fasaha da dabarun aiki domin shawo kan kalubalen da ke kunno kai a harkar jarida.


Masanin, wanda kuma ke jagorantar bincike a Sashen Bincike na Sundiata Post (SPIU) da ke Abuja, ya ce duk da cewa rahotanni, wallafe-wallafe da yada labarai za su ci gaba da kasancewa ginshikan aikin jarida, akwai bukatar kafofin labarai su zurfafa bincike tare da samar da bayanan da ke taimaka wa al'umma wajen fahimtar abubuwan da ke faruwa.


A cikin jawabinsa mai taken “Samfurin Wallafe-Wallafen Sundiata: Gina Dakin Labarai na Afirka Mai Dorewa”, Amuchie ya ce dole ne kafofin labarai su rika yin sharhi da fashin baki, bunkasa ilimi, adana bayanai da gina taskar ilimi da za ta ci gaba da kara musu kima a nan gaba.


Ya yi bayani kan sauye-sauyen da suka faru a harkar yada labarai, tun daga tasirin tallace-tallace da kafafen sadarwa zuwa yadda aikin jarida na yanar gizo ya sauya aikin jarida na takarda, sannan kafafen sada zumunta da fasahar kirkirarriyar basira (AI) suka fara sake fasalin aikin jarida na yanar gizo.


A cewarsa, amfani da AI na bai wa mutane damar samun bayanan da kafofin labarai suka wallafa ba tare da sun ziyarci shafukansu na yanar gizo ba.


Ya ce wannan sauyi ya kamata ya sa mawallafa su sake nazarin yadda za su tabbatar da muhimmancinsu da kuma jawo hankalin masu tallata kayayyaki da ayyuka.


“Me za mu yi domin mu ci gaba da kasancewa masu kima a matsayinmu na mawallafa da kwararrun harkar labarai? Wane abu ne masu tallace-tallace za su duba wajen tantance mu da ba mu talla? Ta yaya za mu samar da kima domin mu ci gaba da kasancewa masu muhimmanci?” in ji shi.


Amuchie ya ce duk da cewa fasaha za ta ci gaba da sauyawa, babban burin aikin jarida na samar da bayanai masu amfani zai ci gaba da kasancewa. Ya jaddada cewa yin fashin baki da bayyana alakar da ke tsakanin abubuwan da ke faruwa na daga cikin muhimman hanyoyin da kafofin labarai za su bi domin dorewa.


Ya bayyana wasu muhimman kadarori da kafofin labarai za su bukaci ginawa a zamanin da ake kira “Zero-Click”, wato lokacin da mutane ke samun bayanai ba tare da danna hanyar shiga shafin da aka wallafa su ba.

Advertisement

NRS Gateway


Daga cikin abubuwan da ya ambata akwai amana, kwarewa da tasiri, ilimi, taskar bayanai, tarihin abubuwan da suka faru, bincike na asali, tsare-tsaren samar da bayanai, adana bayanai, dangantaka da sanayya.


Ya ce wadannan kadarori suna taimaka wa kafofin labarai wajen gina amincin masu sauraro da samar da hanyoyin samun kudaden shiga, ko da kuwa mutane ba sa ziyartar shafukansu kai tsaye.


Ya kuma gabatar wa mahalarta taron wani rahoton bincike na shekarar 2025, wanda aka wallafa a watan Afrilun 2026 karkashin sunan SquirrelPR RANKED Report.


A cewarsa, rahoton ya nuna raguwar yawan ziyartar shafukan labarai na yanar gizo a Najeriya, inda ya ce an samu raguwar kashi 26.2 cikin dari, daga ziyara sama da biliyan daya zuwa kimanin miliyan 769.


Ya ce mafita ita ce kafofin labarai su sauya daga kasancewa wuraren samar da labarai kawai zuwa cibiyoyin samar da ilimi da bayanai masu zurfi.


“Wannan ba yana nufin watsi da aikin jarida ba ne,” in ji Amuchie.


GOCOP Ta Bukaci Mawallafa Su Kware a Fannonin Aiki


Tun da farko, Shugaban GOCOP, Danlami Nmodu (mni), ya ce an shirya horon ne domin taimaka wa mambobin kungiyar fahimtar damar da ke gabansu da kuma hanyoyin bunkasa ayyukansu.


Nmodu ya ce kungiyar na da kwararru da editoci da suka samu nasarori a fannoni daban-daban, wadanda za su iya zama fitattun masana, shugabannin kamfanoni da masu rike da manyan mukamai a matakin kasa da na duniya.


Ya ce mambobin kungiyar na da kwarewa da dabi'u masu kyau da za su iya taimakawa wajen ci gaban al'umma.


Shugaban ya kuma shawarci mambobin da su fara kwarewa a wasu fannoni na musamman domin wallafe-wallafensu su zama abin dogaro wajen samun sahihan bayanai a wadannan fannoni, tare da kara karfafa matsayin GOCOP.


A yayin taron, Nmodu ya kuma tuna da tsohon shugaban GOCOP kuma wanda ya kafa jaridar Eagle Online, marigayi Dotun Oladipo, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin ginshikan kungiyar kuma abokin kowa.


Mahalarta taron sun gudanar da shiru na minti daya domin girmama marigayin a farkon zaman.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 8?