HON. IBRAHIM KABIR MASARI: Mutum mai Dimbin daraja

Wani karin magana na Hausa na cewa, ‘nagari na kowa, mugu na kansa’. Wannan karin magana yana bayyana matsayin halayya da ]abi’a a cikin fahimtar addini da al’adar Hausawa. Ainihin…

Katsina City News September 19, 2026  ·  12:00 AM
| 49 Views
HON. IBRAHIM KABIR MASARI: Mutum mai Dimbin daraja
HON. IBRAHIM KABIR MASARI: Mutum mai Dimbin daraja


Wani karin magana na Hausa na cewa, ‘nagari na kowa, mugu na kansa’. Wannan karin magana yana bayyana matsayin halayya da ]abi’a a cikin fahimtar addini da al’adar Hausawa. Ainihin kimar mutum ba a auna ta da mu}amin da yake kai, dukiyar da yake juyawa, ko abokan da yake tare da su, a’a, ana auna ta ne da irin alherin da yake yi wa mutanen da yake hulɗa da su. A kan wannan mahangar mai ]orewa ne na gamsu cewa Hon. Ibrahim Kabir Masari mutumin kirki ne na gaske.


Kwanan nan wata jarida ta ƙasa ta tuntube ni don in faɗi abin da na sani game da Hon. Ibrahim Kabir Masari, Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Al'amuran Siyasa. Na ba da gajeren yabo, amma daga baya na ji cewa ya kamata na faɗi fiye da haka game da mutumin da na saba da shi sosai tsawon sama da shekaru talatin. Don haka, abin da ke tafe ba kima ba ne kawai bisa mukaminsa na yanzu ko shaharsa ta fili, a'a, ra'ayin wanda ya san shi a matakai daban-daban na rayuwarsa ne.


Wannan bayanin ‘mutumin kirki,’ fitaccen malamin nan Anthony H. M. Kirk-Greene ya yi bincike a kai da zurfin fahimta a lokacin laccarsa ta tunawa da Hans Wolff a shekara ta 1973, wadda daga baya aka wallafa a matsayin littafi a shekara ta 1974. A wurin Kirk-Greene, wannan mahanga ta wuce kawai a yaba wa mutum a matsayin nagari. Wani kima ne na kyawun dukkan halayyar mutum, wanda ke bayyana a cikin mu'amalarsa, zamantakewarsa, hukuncinsa, kamun kansa, da gaskiyar halayyarsa. A fahimtar Hausawa, kirki wani abu ne da dole ne mutum ya rayu da shi kafin a siffanta shi da shi.


Bisa wannan ma'auni mai zurfi ne na san Ibrahim Kabir Masari. Sama da shekaru talatin, na lura da wata ]abi'a mai ban mamaki a tare da shi ta dacewar abin da yake faɗa da abin da yake aikatawa. Ya damu da gaskiya da amana, kuma a zamana da shi ban taɓa ganin ya yi watsi da gaskiya saboda kawai ba ta yi masa daɗi ba. Hakazalika, rike gaskiya da cika al}awari na bayyana a fili wajen mahimmancin da yake ba wa alaƙoƙi da nauyin da aka damƙa masa.


Wannan halayya ta fi fitowa fili a mu’amalarsa da mutane da cibiyoyi. Na kalle shi yana nuna ladabi da mutuntawa ga hukumomi, musamman ma ga sarakunan gargajiya na Katsina da sauran sassan ƙasa. A gaban Gwamnan Jihar Katsina, Sarkin Katsina, Sarkin Daura da sauran sarakunan gargajiya, mu’amalarsa tana nuna gaskiyar mutuntawa ne maimakon siyasa kawai. Akwai fahimta a tare da shi cewa iko yana ɗauke da kimarsa, kuma mutunta cibiyoyi alama ce ta cikar halayya.


Duk da haka, ainihin tsagwaron halayyarsa tana fitowa fili ne a wajen tarrurruka na ƙashin kai. Masari yana hulɗa cikin sauƙi da 'yan uwa da dangi, talakawa da 'yan siyasar karkara, kamar yadda yake hulɗa da gwamnoni, 'yan majalisa, manyan jami'ai, da 'yan siyasa na ƙasa. Ba ya buƙatar wani taro na musamman don ya nuna muhimmancinsa. Akwai karsashi da gaskiya a hulɗarsa da mutane, kuma wannan ikon riƙe alaƙa a matakai daban-daban na al'umma ya kasance ɗaya daga cikin manyan alamomin rayuwarsa ta siyasa.


Haka kuma yana da basirar gano nagarta da damar mutane. A lokuta daban-daban, ya fahimci }warewar mutane kuma ya taimaka wajen buɗe musu ƙofofi; fitowar mutane irin su Engr. Muttaqa Rabe Darma misali ne ɗaya da yake zo min a rai. A gare ni, wannan yana nuna wani muhimmin ɓangare na hikimar siyasa: ba kawai gane wanda ke da shahara a yau ba, har da hango wanda zai iya yin hidima mai fa'ida a gobe.


Karamcinsa da karɓar baƙi wata dama ce da na sha cin karo da ita tana maimaituwa. Na ga an nuna hakan ba kawai ta hanyar karamci na ƙashin kai ba, har ma ta hanyar burinsa na tallafa wa mutane, cibiyoyi, da abubuwan da yake gani suna da muhimmanci. Taimakonsa a ɓangaren ilimi, gami da gagarumin gudummawar da ya bayar wajen kafa Jami'ar Musulunci a yankin da ke matukar buƙatar ta, na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi fitowa fili na irin halin da yake da shi tun kafin ya samu wannan shahara ta siyasa ta yanzu. Wannan aiki ba shi kaɗai ba ne, domin ya aikata abubuwa masu yawa na alheri a baya can da ma daga baya. 


Sai dai abin takaici, maimakon yabo, sai ma maganganu na soki-burutsu daga 'yan adawa. Kamar yadda ake zato, wannan haushi bai fito daga karamcin da kansa ba, a'a, daga kishi da kyashi na siyasa ne. Masu sukar sa sun zaɓi haɗa wannan abin da muhallin siyasa da tattalin arzi}in dukiyarsa, ta hanyar ƙirƙirar jita-jitar cewa ya tara ta ne ta hanyar zalunci ko goyon bayan siyasa, suna satar kallon karamcin a matsayin dabarar siyan goyon baya maimakon tsagwaron alheri. Na tsaya tsayin daka wajen cewa babu ɗaya daga cikin waɗannan da ke shafar Hon. Ibrahim Kabir Masari.


Advertisement

NRS Gateway

Rayuwar fili, a zahiri, tana zuwa da nata rukunin matsaloli. Alaƙoƙin siyasa suna iya karɓar tasiri daga buƙatu, tsammani, da mabambantan ~angarori, kuma Katsina ba ta tsira daga irin waɗannan matsin lamba ba. An samu fahimtar bambance-bambance tsakanin buƙatun siyasa da ke da alaƙa da Hon. Masari da na Gwamna Dikko Umar Radda.


Na sami damar yin magana da dukkan su - Gwamna Radda da Hon. Masari kan waɗannan bambance-bambance da aka ruwaito, kuma kowannen su ya tabbatar mini cewa, su abokan juna ne kuma abokan haɗin gwiwa ne a tafiya guda tun da daɗewa, ta yadda dukkan maganar samun saɓani mai tsanani tsakanin su kawai tunanin fatan alheri ne na 'yan gaza-gani. Mutane na iya cewa irin wannan faɗar 'babu matsala' ita kanta siyasa ce. Sai dai a gare ni, hanyar da Hon. Masari ke karɓa da mi}a wuya ga Gov. Radda a matsayin Jagoran APC na Jihar Katsina, da hanyar da Gov. Radda ke ba Hon. Masari girma da mutuncin da ya dace da shugaban APC na ƙasa kuma mai riƙe da babban mu}amin siyasa, bayyanannen shaida ne na mutunta juna a tsakanin su. Lallai, 'yan adawa na gida suna ƙoƙari sosai don ƙirƙirar jita-jita ta saɓani da jingina abubuwan da ke faruwa a Katsina ko ga shugabancin jihar ko ga abokan hulɗar Masari. Dukkan waɗannan dabarun siyasa ne, saboda babu irin wannan saɓanin. Abin da duk shugabannin biyu da abokan aikinsu ke da shi a gabansu buri ne guda ɗaya: tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gov. Radda da dukkan 'yan takarar APC sun samu nasara gagaruma a zaɓuka masu zuwa a Katsina da daukacin Najeriya.


Wannan kamun kai yana haɗuwa ne ta hanyar halitta da wata ]abi'ar da nake alaƙanta ta da Masari: haƙuri da yafiya. Rayuwar fili tana tafe da suka, saɓani, da rashin fahimta, amma ya fi karkata wajen yin haƙuri maimakon ma'amala da rigima, da kuma yin haƙuri maimakon muhawara ta fili mara amfani. A zamanin da rayuwar fili ke fa'idantuwa da hayaniya, irin wannan natsuwa tana da sauƙin rasawa; duk da haka, tana nan a matsayin natsuwar halayya.


Tasirinsa na siyasa shi ma ya fi bayyana ta hanyar alaƙa maimakon kaye-kaye. Ya gina alaƙoƙin da suka ba shi damar haɗa mutane guri guda, buɗe ƙofofi, da samar da damammaki ga mutane daga Katsina da sauran sassan Arewacin Najeriya. A ɓangaren jawo mutanen Arewa kusa da Shugaban Ƙasa ta fuskar taimakon siyasa—na]in mu}amai, ayyukan yi, da damar kasuwanci—ban tsammanin akwai wanda ya wuce shi. Ko da wane ra'ayi ne mutum ke da shi a siyasa, ikon gina da riƙe alaƙa a mabambantan rukunai na tasiri babbar hanya ce ta kimarsa a fili.


Dukkan waɗannan siffofi suna mai da ni ne ga ‘mutumin kirki’, saboda wannan kalmar tana tamfatsa tambayar da ta fi zurfi fiye da nasarar siyasa: wane irin mutum ne shi idan aka cire mu}amin? Bayan sama da shekaru talatin na sanin Hon. Ibrahim Kabir Masari, na ga mutumin da ya amince da muhimmancin alaƙoƙi, yake mutunta dattiɓai da cibiyoyi, yake kyauta gwargwadon ikonsa, yake gane }warewa, yake haƙuri a ƙarƙashin matsin lamba, kuma yake ba da muhimmanci sosai ga amana.


A yau, yana riƙe da muhimmin matsayi a rayuwar siyasar Najeriya a matsayin Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Al'amuran Siyasa. Mu}amin yana kawo shahara, tasiri, da nauyi, amma mu}amai masu shuɗewa ne. Gwamnatoci suna canzawa kuma naɗe-naɗe suna ƙarewa. Abin da ke ]orewa shi ne halayyar mutumin da ya riƙe mu}amin da kuma irin tuna shin da yake bari a rayuwar waɗanda ya yi tafiya tare da su.


Wannan ne ya sa nake komawa ga tsohuwar hikimar Hausa: ‘nagari na kowa’. A gare ni, Ibrahim Kabir Masari ba ana bayyana shi ba ne ta hanyar kusancinsa da iko ko shaharar mu}aminsa. An fi fahimtar sa ta hanyar abubuwa na sirri: Alaƙoƙin da yake riƙewa, amanar da yake ɗauke da ita, mutanen da yake taimakawa, cibiyoyin da yake mutuntawa, }warewar da yake gani, da kuma kamun kansa a tafiyarsa.


A ƙarshe, lakabi na iya faɗa muku inda mutum ya tsaya, amma halayya tana faɗa muku wane ne shi. Mu}amai suna iya sanya mutum a tarihi, amma rayuwar da ya taɓa tana ƙayyade yadda za a ri}a tunawa da shi. Bayan shekaru daban-daban guda talatin na kallon irin rawar da Ibrahim Kabir Masari yake takawa a cikin yanayi mai canzawa na rayuwar jama’a, zan iya faɗi, da }warin gwiwar sani na ƙashin kai maimakon dacewar siyasa, cewa bayanin da ya fi kusa da mutumin da na sani shi ne wanda aka tsamo daga hikimar al'ummarmu: ‘mutumin kirki’ - wato nagari.


Sanata Ibrahim M. Ida, Ph.D., CON

Wazirin Katsina

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 7?