LABARIN 'YA'YAN MAI FASKARE: Gajeren Labarin koyar da kyakkyawar dabi'a.
- Katsina City News
- 08 Sep, 2023
- 1196
Wani Injiniya ne ya dauki hayar wani mai faskare don ya sare duk itatuwan da ke farfajiyar gidansa. Yadin gidansa ya yi duhu ne sosai saboda an lulluɓe shi da ganye, don haka yana son barin hasken rana ya shigo gidan sosai.
"Yanke su kamar katako, sa'an nan kuma ka matsar da katakon zuwa wancan gefen shingen, zan sami wanda zan saya," in ji Injiniyan, ya ce wa mai faskaren.
Washegari da safe, mai faskare ya zo da ’ya’yansa maza biyu don su soma aikin ranar. Za su yini ne cikin tsanani na sare itatuwa guda goma, kuma a yanka su gungume-gungume, sannan a kwashe su zuwa wani wurin daban.
Sa’ad da mai faskaren ya shirya aikinsa yana jera kayan aikin da zai bukata, Injiniyan yana kallon su ta taga daga ɗakin kwanansa. Bai motsa ba ya zauna kan kujera yana zuba musu ido.
Ya lura cewa ƙaramin ɗan mai faskaren ba ya yin wani aiki. Yaron bai taimakon mahaifinsa da ɗan'uwansa ta kowace hanya ba. Ya zauna a kusurwar bangon gidan ne kawai yana cin 'ya'yan tuffaha, yana kallon su suna yin aikin faskaren su kadai. Ran Injiniya ya yi dubu ya baci saboda abin da yake gani na kasala da son kai na yaron. "Wannan yaro akwai dan banzan yaro!" ya yi ba'a ya rufe taga.
Da maraicen ranar, mai faskaren ya je wajen Injiniyan. Da alama ya gama aikinsa. Cike da gajiya ya ce masa:
"An gama yallabai! Zan iya samun biyan kuɗin aikina, kamar yadda muka tattauna a kan wannan aikin?"
Bayan ya duba farfajiyar, Injiniyan ya ji daɗin aikin da aka yi a wurin. Yana shiga gidan ya fito da wasu kudi ya mika wa mai faskaren. Sannan ya sa hannu a aljihu ya zaro agogon hannu mai tsada. Ya ce, "Ina so ka ba da wannan agogon ga babban danka ... kyauta ce a gare shi. Shi yaro ne mai ban mamaki sosai, saboda yadda ya taimake ka ka yi dukkan aikin. Na san, wata rana za ka yi alfahari da shi".
Ya dakata na dakika, sannan ya ci gaba. "Shi kuma dayan na ki...Na ji takaicin halinsa, bai nuna sha'awar yin aiki ba, kuma ba shi da sha'awar yin abin kirki, gara ka gyara masa zama tun yanzu ko ya girma ya zama mutum mara tarbiyya kuma maras sanin ciwon kansa"
Fuskar mai faskaren ta canza da sauri cikin wani yanayi mai tunani. Sannan ya ce:
“Yallabai, akwai wani abu da kake bukata ka sani game da dana karamin nan. A gaskiya shi yaro ne mai kuzari da aiki tukuru, ya fi yayansa ma aiki tukuru, amma a ‘yan watannin da suka gabata ya kamu da ciwon koda, wanda hakan ya kai ga yi masa aiki don cire daya daga cikin kodarsa. Domin samun lafiyar sauran kodar, likitoci sun yi gargadin cewa kada ya yi wani aiki mai tsanani. Shin ka gan shi yana cin tuffa? Ai yana ci ne saboda 'ya'yan itacen suna da sanadarin fiber da kuma abubuwan da ke hana kumburi, wanda kan taimaka wajen inganta aikin koda"
Da jin haka, sai Injiniyan ya ji tausayi da kuma nadama. Zuciyarsa ta matse a kirjinsa. Sannan ya furta cikin karyewar murya, "Wannan hali dole ne ya yi masa tsanani, ku yi hakuri da hukuncin da na yanke wa danku. Kamata ya yi na fara da yi masa tambayoyi, maimakon yanke masa hukunci. Lalle ne, ba za mu taba yanke hukunci a kan littafin daga kallon bangonsa ba... Yanzu, na yi tunanin yaron nan ya cancanci wani abu fiye da agogon hannu, jira na daƙiƙa kawai ... Zan samo masa wani abu na musamman".
Darasin labarin: Kada ka yanke hukunci ko yin zato, har sai ka san cikakken labarin abu. Idan kana shakka, tambayi mutumin da abin ya shafa kai tsaye. Tambayoyi suna kawar da rudani kuma suna sa mu a shafi guda kan kowane batu. Yi magana da wadanda abu ya shafa a sarari iya yadda za ka iya don guje wa rashin fahimta. Kasance mai bincike, amma ba mai yanke hukunci ba.
Daga Shafin Ibrahim Musa
Marubuci: Chima_Dickson dan Jarida