SHEKARU 24 DA GUSHEWAR DOKTA MAMMAN SHATA KATSINA: HAR YANZU BUWAYARSA BA TA GUSHE BA
- Katsina City News
- 18 Jun, 2024
- 658
A. I. Kankara
A yau, Talata, 18/6/2024, Duniya ta na sake yin juyayin cika shekaru 25 da rasuwar Alhaji Dokta Mamman Shata Katsina. Mu na yi ma sa addu’a, Allah Ya daxa kyautata makwanci, Allah Ya gafarta ma sa. Shekaru da dama bayan rasuwarsa, abubuwa tara (9) da su ka zame ma Shata gatancin da babu wani fitaccen mutum a Afirka da ya same su, su ne:
Har yanzu, har kuma gobe Duniya ta kasa mantawa da shi saboda shahararsa da buwayarsa da baiwarsa.
Har yanzu, har kuma gobe, Shata na xaya daga cikin mutanen da aka fi yin bincike a kansu a Duniya, ta fuskar adabin zamani da na gargajiya da al’adu da rayuwar Bahaushe.
Har yanzu, har kuma gobe jama’a masoyansa a ko’ina a cikin Duniya ba su daina yi masa addu’a ba,
Har yanzu, har kuma gobe ba’a daina sauraren waqoqinsa ba, wasu sabbi ma na ta fitowa kullum, sannan,
Har yanzu, har kuma gobe buwayarsa a fagen waqar Hausa ta na nan kamar ma ya na raye, savanin sauran mawaqan Qasar Hausa, da sun gushe sai al’amarin waqarsu ya ragu.
Har yanzu, har kuma gobe, Shata ne kaxai daga cikin mawaqa da aka samu, shekarunsa na rasuwa na qaruwa, maimakon mantawa da shi ta qaru, sai, kullum, yara qanana na ta tasowa ma su son jin waqoqinsa da tarihinsa.
Har gobe kafafen watsa labaru su na amfani da waqoqin Shata wajen gabatar da muhimman abubuwan da su ka faru ko su ke faruwa a cikin Qasa.
Shata kan ambaci abu a cikin waqa sai kuma bayan wasu shekaru da dama a ga abubuwan su na faruwa a hankali. Ga su nan rututu a cikin waqoqinsa.
Mafi yawancin waqoqinsa na Siyasar Qasa (gwarzayen waqoqi) da ya yi, ya na yin gargaxi kan gyaran Nijeriya na matsaloli da su ka, ko ya ke hasashen tasowarsu, a yau ga su mun gani su na ta faruwa.
Amma, idan mu ka waiwaya, bayan shekaru 24 da rasuwarsa, Mamman Shata ya kasa samun abubuwa guda biyar (5) kuma daga gwamnatocin Qasarnan, duk da kiraye-kirayen da ake yi na tsawon lokaci. Abubuwan su ne:
Har yanzu, har kuma gobe, gwamnatin Tarayya ta kasa yin wani abu muhimmi a cikin Qasa wanda za ya kasance abin tuna Shata ne, na dindindin. Don haka, gaskiya, gwamnati ba ta martaba shi ba, ba ta yi ma sa adalci ba.
Har yanzu gwamnatin jihar Katsina, mahaifarsa, ko ta Tarayya, ko wata jami’a ko wata cibiyar bincike, ta/sun kasa samun wata cibiya ingantatta wadda za ta tattara kayan tarihin Shata musamman domin tunawa da shi, don bincike da nazari da kuma ma su yawon shaqatawa ko ziyara, ko ma su yawon buxe ido. Sai a tattaro duk abin da ya shafi Shata, a amsa a kuma gyara shi, sannan a yi ma sa adanawa mai kyau don dalilan da na ambata a sama. Tun cikin 1999 ya kamata a ce an fara yin haka don kada abubuwansa su yi nisa. Amma dai, a yanzu xin ma, wuri bai qure ba, idan an so yin hakan.
Har yanzu gwamnatin Katsina, ko ta Tarayya sun kasa amsar gida ko mahaifar Shata, ko gidansa na Funtuwa su mayar da shi/su cibiya ko santa ta bincike, kamar dai yanda gwamnatin ta yi ma gidajen Malam Aminu Kano (jagoran jam’iyyun NEPU da PRP) da kuma firimiyan jihar Arewa, Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto)
Har yanzu, cibiyar bincike akan ilimi, walwalar jama’a da al’adun gargajiya na Qasashen Duniya watau UNESCO (reshen Majalisar Xunkin Duniya) ta kasa amsar Shata kacokan a matsayin kayan tarihi don ta mayar da al’amarinsa a cikin abubuwan da za ta rinqa kula da su. Yakamata UNESCO ta mayar da hidimar Shata xaya daga cikin kayan tarihi na Duniya. Alal misali: maqabartarnan mai tarin tarihi da ke a Timbuktu a Qasar Mali, ita wannan cibiya ke kula da wurin.
Yakamata a haxe qungiyoyi na sa-kai da ake da su akan Shata su koma mai inuwa xaya. Dunqulewarsu za ya sanya hukumar UNECSO ko hukumar Majalisar Xunkin Duniya ta, ko su shigo su amshi Shata, su adana abubuwansa, da su ka shafi gidansa, mahaifarsa da sauransu.
Mu na fata Allah Ya gafarta ma Dokta Mamman Shata Katsina, Ya gyara bayansa, Ya shirya ma sa zuriyarsa. Ina miqa gaisuwata ga ‘Na Izzatu mai benen bene, amma benen duk na waqa’.
Daga Hagu: Kankara tare da ‘ya’yansa, a Qofar gidan su Shata daga gabas, inda mahaifin Shata kan ajiye
kadoji, 15/4/2014 ; Hagu: Qanqara tare da marigayiya Hajiya A’isha (Yalwa) Yakubi Shendam, 2015
Tsakiyar gidan su Shata, Musawa, 2014 ; Dama: Gidan gonar Shata a Musawa, ‘Gidan Marke’, 2014
Wani vangare na ‘Gidan Marke’ inda Shata kan yi fayafayi; Dama: Shata tare da Gamar Haxejiya, 1999
Farfesa Aliyu Ibrahim Kankara ya rubuto daga birnin Katsina,
Talata, 18/6/2024.
aibrahim@fudutsinma.edu.ng/ialiyu260@gmail.com/ 07030797630/08144196845.