"Mun ɓullo da wani tsari da zai rage shigo da baƙin Motoci, na sata a jihar Katsina...NATA
- Katsina City News
- 26 Aug, 2023
- 852
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kungiyar Kanikawa ta ƙasa reshin jihar Katsina wato (Nigerian Automobile Technician Association) NATA, a karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar na jihar Katsina Injiniya Abbati Muhammad, ya bayyana haka a lokacin da Katsina Times take zantawa dashi.
Injiniya Abbati ya bayyana Irin tsare-tsare da suke dashi da zai taimawa jihar Katsina da kuma shirin daukar Matasa dubu uku Aiki don rage zaman banza.
Injiniya ya bayyana cewa duk yaro matashi da ya koyi Aikin gyaran Motoci, ko mashina da sauransu a rana zai iya aikin dubu biyar, yace "wannan kau bansan ba wane irin aikin gwamnati bane zaka samu a matakin farko ko na biyu har zuwa na uku, ace a wata kana kwasar dubu 150" yace to mu a aikin mu na wannan sana'ar madamar ka tsaya ka koya kuma ka iya zaka samu fiye da haka ma.
Injiniya Muhammad yayi godiya ga Gwamnatin jihar Katsina akan yanda ta samar masu da fili wanda za a tattare masu sana'ar waje guda kuma a koyar dasu, ilimin sana'ar a zamanance, yace duba da yanda yanzu motocin duk sun koma Kwamfuta, don haka gwamnati tace zata gina wajen koyar da ilimin gyaran kuma har an samar da wajen yace "muna godiya da kuma kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta maida hankali kuma ta waiwayi aikin don a kammalashi cikin sauri.
Da Katsina Times take Tambayarsa game da Nasarorin da kungiyar ta samu, Abbati ya bayyana cewa sun samar da wani tsari a ilimance da zai rage shigo da motocin sata a jihar Katsina inda ya bayyana wani kundi na zai tattara dukkanin bayanan Motar da abinda ta kumsa, kuma ko wane gareji yace zasu samar da irin wannan kuma sunje ga hukumomin tsaron sun karamasu ilimi bisa ga nasu ta hanyar da zasu iya damƙewa da gano bakin motocin sata.
Yace suna nan suna gyare-gyaren kuma nan da dan lokaci tsarin zai fara aiki.
Yace "Mun samar da tsarin gudanarwa na shugabanci wanda ada ba'a haka amma zuwanmu yasa yanzu kungiyar tana shirya zabe kuma tana da wakilai a dukkanin fadin jihar Katsina, kuma cikin hadin kai da tsari.
Tattaunawar da Katsina Times tayi da Shugaban na Kanikawan jihar Katsina a ranar juma'a ta nadi Bidiyon tattaunawar wanda muka sanya a kafafenmu na sada zumunta wanda zaku iya gani kaitsaye.