An Gurfanar da Aminu Nasta a Kotu Bisa Zargin Lalata Hoton Shugaban Kasa da Satar Naira Miliyan 35

Daga Wakilanmu @ Katsina TimesAn gurfanar da Aminu Nasta a wata kotu da ke Abuja bisa zargin lalata wani allo mai ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa, da kuma balle wani…

Katsina City News September 02, 2026  ·  12:00 AM
| 236 Views
An Gurfanar da Aminu Nasta a Kotu Bisa Zargin Lalata Hoton Shugaban Kasa da Satar Naira Miliyan 35
An Gurfanar da Aminu Nasta a Kotu Bisa Zargin Lalata Hoton Shugaban Kasa da Satar Naira Miliyan 35



Daga Wakilanmu @ Katsina Times


An gurfanar da Aminu Nasta a wata kotu da ke Abuja bisa zargin lalata wani allo mai ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa, da kuma balle wani ofishin jam’iyyar APC tare da yin awon gaba da kuɗaɗen da aka ajiye a ofishin, waɗanda yawansu ya kai Naira miliyan 35.


A cewar rahoton jaridar Sahara Reporters, Aminu Nasta ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da zargin cin amanar ƙasa da kuma sata.


Nasta ya bayyana cewa shi ne shugaban wata ƙungiya da ke kare martabar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Dikko Umar Radda, yana mai tambayar dalilin da zai sa ya aikata irin waɗannan laifuka.


Lauyoyin Nasta sun kalubalanci tuhumomin da aka gabatar a kansa tare da neman kotu ta bayar da belinsa.

Advertisement

NRS Gateway


Sai dai, lauyoyin masu gabatar da ƙara sun nemi kotun ta ba su ƙarin lokaci domin su ci gaba da tsare Nasta na tsawon makonni biyu, domin kammala binciken da suke gudanarwa.

Har zuwa lokacin da aka ɗage zaman kotun a ranar Talatar da ta gabata, kotun da ke Jiwa, a Babban Birnin Tarayya Abuja, ba ta bayar da belin Aminu Nasta ba.


Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page.katsina city news 

Facebook .jaridar Taskar labarai 

All social media handles @ katsina times 

07043777779.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 7?