Matsalolin ‘One Chance A Abuja: An nemi karin Tsaurara Tsaro

KatsinatimesWasu waɗanda suka sha fama da hare-haren ’yan fashi masu amfani da motocin haya wajen aikata laifin da ake kira “One Chance” a yankunan Dei-Dei da Kubwa da ke Abuja,…

Katsina City News August 27, 2026  ·  12:00 AM
| 37 Views
Matsalolin ‘One Chance A Abuja: An nemi karin Tsaurara Tsaro
Matsalolin ‘One Chance A Abuja: An nemi karin Tsaurara Tsaro

Katsinatimes


Wasu waɗanda suka sha fama da hare-haren ’yan fashi masu amfani da motocin haya wajen aikata laifin da ake kira “One Chance” a yankunan Dei-Dei da Kubwa da ke Abuja, sun yi kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro domin dakile matsalar.


Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun bayyana hakan ne a tattaunawar da suka yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata.


Ana amfani da kalmar “One Chance” wajen bayyana salon fashi ko satar mutane da ƙungiyoyin masu laifi ke yi, inda suke yaudarar matafiya su shiga motocinsu, kafin su yi musu fashi, duka ko kuma tilasta musu ba su kuɗi da wasu kayayyaki masu daraja.


Wata ma’aikaciyar gwamnati a Kubwa, Misis Blessing Umeh, ta ce an yi mata fashi ne bayan ta shiga motar haya da take zaton za ta kai ta inda take son zuwa.


“Na shiga motar da yamma, ina tunanin motar haya ce ta yau da kullum. Bayan ’yan mintuna, mutanen da ke ciki suka yi min barazana tare da kwace wayata, kuɗi da katin ATM.


“Sun tilasta min na bayyana musu lambar sirrin ATM dina, suka kwashe kuɗin da ke asusun bankina, sannan suka jefar da ni a wani wuri da ba kowa,” in ji ta.


Ta ce abin da ya faru ya jefa ta cikin mummunan yanayi na tsoro da damuwa wanda ba za ta manta da shi ba.


Wani mazaunin Dei-Dei, Mista Emeka Okeke, shi ma ya ce an kai masa hari ne lokacin da yake dawowa daga wurin aiki.


Ya ce ’yan fashin sun kwace masa waya, kwamfuta tafi-da-gidanka da wasu kayayyaki masu daraja.


“Tun daga lokacin nake jin tsoron shiga motocin haya, musamman da dare.


“Gwamnati ya kamata ta ƙara yawan sintiri da jami’an tsaro, tare da tabbatar da cewa an kama waɗanda ke aikata irin waɗannan laifuka kuma an gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.


Wata mata, Aisha Ibrahim, ta ce ta tsira daga fadawa tarkon One Chance ne bayan ta fara zargin halayen wasu fasinjojin da ke cikin motar.


Advertisement

NRS Gateway

Ta ce ta nemi direban ya tsaya domin ta sauka kafin motar ta yi nisa.


“Na lura da wasu abubuwa da suka sa na fara zargi, don haka na nemi a sauke ni. Na yi sa’a na tsira, amma mutane da dama ba sa samun irin wannan damar,” in ji ta.


Aisha ta yi kira da a samar da ƙarin wuraren binciken ababen hawa da kuma inganta sa ido kan motocin haya domin kare fasinjoji.


Wasu mazauna yankunan sun ce yawaitar hare-haren One Chance na ƙara sanya tsoro a zukatan jama’a, lamarin da ya sa wasu ke guje wa yin tafiye-tafiye da dare.


Shugaban wata al’umma a Dei-Dei, Malam Usman Sani, ya shawarci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsantsan tare da gaggauta kai rahoton motocin da suke zargi ko wasu abubuwan da ba su saba gani ba ga hukumomin tsaro.


Ya ce ya kamata a ci gaba da wayar da kan jama’a domin taimaka musu wajen gane dabarun da masu aikata One Chance ke amfani da su.


Mista Sani ya kuma yi kira ga hukumomi da su tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da ake ganin suna da rauni, tare da inganta tsarin gaggawar amsa kiran neman agaji.


Shi ma wani direban haya, Mista Ikenna Ohia, ya buƙaci hukumomi da ƙungiyoyin sufuri su tsaurara matakan rajista da sa ido kan motocin haya.


Ya ce hakan zai taimaka wajen hana masu aikata laifi fakewa da sunan direbobin haya.


A cewarsa, samar da ingantaccen tsarin tantance direbobi zai bai wa fasinjoji damar bambance sahihan direbobin haya da masu aikata laifi.


Mazauna yankin sun kuma shawarci matafiya da su guji shiga motocin da ba su da cikakken bayani a kansu, musamman waɗanda ke ɗaukar fasinjoji a wuraren da ba su da cunkoso.


Sun kuma bukaci matafiya su riƙa sanar da ’yan uwa ko abokai bayanan tafiyarsu a duk lokacin da hakan ya yiwu.


Haka kuma, sun yi kira ga Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA), hukumomin tsaro da ƙungiyoyin sufuri da su ƙara sintiri, inganta tattara bayanan sirri da wayar da kan jama’a, tare da ɗaukar tsauraran matakai kan masu amfani da motocin haya wajen aikata laifuka.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 4 + 9?