Daga Yusuf Hassan Buhari
A safiyar Talata 26 ga Sha'aban 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga Fabrairu 2025, an gudanar da bikin karrama Shugaban Kwamitin Aminattu na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), kuma Daraktan Da'awah na ƙasa, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah).
Jami’ar European-American University ce ta ba shi wannan girmamawa ta Digirin Digirgir (Honorary Doctorate Degree) a wurin taro na Open University da ke kan hanyar Katsina zuwa Kaita.
An haifi Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina a shekarar 1947 a garin Gwaram na Jihar Jigawa. Ya sadaukar da rayuwarsa ga neman ilimin addinin Musulunci, fiqihu, da gyaran zamantakewa.
Tun yana matashi, Sheikh Sautus-Sunnah ya nuna ƙwazo a fagen karatun addini. A ƙarƙashin jagorancin kawunsa, Malam Mahmud Dawakin Zage Kano, babban malamin Malikiyya, ya haddace Alƙur’ani, tare da kwarewa a fannoni kamar Fiqhu, Tauheed, Sirah, Tajwidi, da Falsafar Musulunci. Daga nan ya ci gaba da zurfafa iliminsa a ƙarƙashin kulawar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, tsohon Grand Khadi na Arewacin Najeriya.
Sheikh Sautus-Sunnah ya yi karatu a Kwalejin Horar da Malamai ta Larabci da Islamiyya da ke Katsina, inda ya zama gwarzon dalibi a shekarar 1983. Bayan haka, ya samu Diploma a fannin Shari’ar Musulunci daga Katsina Polytechnic, inda ya yi fice a karatunsa.
Baya ga karatu, Sheikh Sautus-Sunnah ya kasance babban mai da’awa tun daga shekarun 1970. Ya yi aiki a karkashin Jama’atu Nasril Islam a matsayin mai wa’azi. A lokacin da ya zauna a Kafanchan, Jihar Kaduna, ya kafa makarantar Islamiyya don inganta ilimin Musulunci a yankin, tare da hadin gwiwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da wasu manyan malamai.
Sheikh Sautus-Sunnah na daga cikin mabobin farko da suka kafa Kungiyar JIBWIS, wacce ke fafutukar kawar da bidi’o’i da suka saba wa Musulunci tare da karfafa bin Sunnah. A Jihar Katsina, ya kafa makarantu da dama da suka haɗa da Riyadhul Qur’an da Sautus Sunnah International Comprehensive Schools, inda malamai da kwararru suka samu horo a yammacin Afirka.
Sheikh Sautus-Sunnah ya taka muhimmiyar rawa a ƙarfafa mata da manya ta hanyar ilimi, tare da yakin neman karɓuwar hijabi ga mata Musulmi a Arewacin Najeriya.
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina yana da manyan mukamai a fagen addini, ciki har da:
Sheikh Sautus-Sunnah yana daga cikin Musulmai 500 mafi tasiri a duniya tun daga shekarar 2019 zuwa 2024, wanda cibiyar Royal Islamic Strategic Studies Centre ta Jordan ke fitarwa kowace shekara.
Har ila yau, ya gabatar da kasidu da dama a taruka na ilmantarwa da kuma shirin gyaran al’umma ta hanyar wa’azi da rubuce-rubuce.
Bayan karramawar, Sheikh Sautus-Sunnah ya yi godiya ga Allah (S.W.A) bisa wannan matsayi da ya kai shi. Ya kuma mika godiya ga shugabannin JIBWIS na jiha da kananan hukumomi, tare da dukkan 'yan uwa da abokan arziki da suka halarci wannan taro.
Fans
Fans
Fans
Fans