KIWON LAFIYA: Amai da Gudawa, Kwayoyin Cututtuka da Yadda Ake Kariya
- Katsina City News
- 15 Dec, 2024
- 184
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Menene Amai da Gudawa?
Cutar amai da gudawa, wadda aka fi sani da kwalara da atini, na faruwa ne idan mutum ya kamu da kwayoyin cuta wadanda ke kawo matsaloli a hanji. Ana daukar su ta hanyar ci ko shan abubuwan da suka gurɓace ko kuma ta hanyar ma’amala da mai dauke da cutar.
Alamomin Kwalara
1. Matsanancin gudawa mai ruwa.
2. Amai ba kakkautawa.
3. Bushewar fatar jiki.
4. Fadawar idanuwa da sanyi a jiki.
5. Saukar jini (hypotension).
Illolin Kwalara
- Rashin ruwa a jiki wanda zai iya kaiwa ga mutuwa idan ba a samu agaji ba.
Yadda Ake Kariya
1. Kula da tsabtace jiki da muhalli.
2. Wanke hannu kafin cin abinci ko bayan amfani da bayan gida.
3. Kula da abinci ta hanyar tsaftace shi kafin amfani.
4. Yin amfani da ruwan da aka tafasa ko aka tace domin sha.
5. Kebe masu fama da cutar daga sauran mutane.
6. Sanar da hukumar lafiya cikin gaggawa idan an samu annoba.
Atini: Bacilla da Amiba
Atinin Bacilla (Bacillary Dysentery)
Wannan nau’i na atini kwayoyin cutar Bacilla ke haddasawa. Ana daukarta ta hanyar:
- Shan ruwan sha ko cin abinci da suka gurɓace.
- Yin ma’amala da bayan gida wanda ba a tsaftace shi ba.
- Taba kayan mai dauke da cutar.
Alamomin Atinin Bacilla
1. Gudawa mai gauraye da jini da majina.
2. Ciwon ciki mai tsanani.
3. Tashin zuciya da amai.
4. Bushewar fata da rashin ruwa a jiki.
5. Dandaka da rashin kuzari.
Illolin Atinin Bacilla
- Kumburewar dubura.
- Rarakewar 'yan hanji.
Atinin Amiba (Amoebic Dysentery)
Wannan nau’in atini kwayoyin cutar Amiba ke haddasawa. Ana daukarta ta hanyar:
- Shan gurbataccen ruwa ko cin ‘ya’yan itatuwa marasa tsabta.
- Rashin kula da tsafta.
Alamomin Atinin Amiba
1. Gudawa mai ruwa-ruwa da majina.
2. Ciwon ciki da zai tsananta lokaci zuwa lokaci.
3. Fadawar idanuwa da bushewar fata.
4. Rashin sha’awar abinci da rama.
Illolin Atinin Amiba
- Ciwon hanta.
- Mutuwar dubura ko rashin aiki.
Bambancin Bacilla da Amiba
1. Atinin Bacilla yana tare da gudawa mai dauke da jini da majina, yayin da Atinin Amiba ke dauke da majina kawai.
2. Bacilla yana tafiya ba tare da kugin ciki ba, amma a Amiba kugin yana faruwa kafin ko yayin gudawa.
Riga-kafin Kamuwa da Atini
1. Tsaftace muhalli da jikinka.
2. Wanke hannu bayan amfani da bayan gida ko kafin cin abinci.
3. Tace ruwa, tafasa shi, ko amfani da alif a abinci domin kariya.
4. Kebe masu dauke da cutar daga sauran jama’a.
5. Sanar da hukuma idan an gano annobar cutar.
Tushe
Littafin "Kula da Lafiya" na Safiya Ya’u Yemal.