Shawarwari Bakwai Ga Masu Rataya Jakar Baya Domin Kiyaye Ciwukan Jiki.
- Katsina City News
- 23 Nov, 2024
- 226
Goya jakar baya musamman tsawon awanni na iya zama sababin ciwukan jiki kamar ciwon wuya, kafaɗa da baya. A wani lokacin ma idan maratayan jakar suka shaƙe jijiyoyin laka a wuya hakan na iya janyo rauni ko shanyewar hannu.
Duba shawarwari 7 ga masu rataya jakar baya domin magance waɗannan ciwukan jiki.
1. Zaɓi maratayan jakar baya masu faɗi da kauri sannan kuma su kansance masu taushi. Duk wannan zai taimaka kada maratayan jakar su riƙa cin jiki. Domin idan maratayan jakar suna cin jiki, hakan na nuni da haɗarin shaƙe jijiyoyin laka da jijiyoyin jini a wuya ko kafaɗa.
2. Rataya maratayan jakar duka biyun, saɓanin rataya hannu ɗaya kawai. Domin rataya maratayi ɗaya kawai na janyo tasgaɗewar kafaɗa da gadon baya saboda rinjayen nauyin jakar.
3. Kada a maƙare jakar da kayayyaki fiye da ƙima. An fi son nauyin jakar kada ya wuce kaso 15 cikin 100 na nauyin jikin mutum.
Misali, idan nauyin mutum ya kai kilogiram saba'in (70Kg) a kan ma'aunin nauyi; to nauyin jakar ya kamata ya kasance kilogiram goma da rabi (10.5Kg).
4. Yayin da jakar ke rataye, an fi so ta kasance tsakanin ƙasa da kafaɗun da kuma sama da ƙugu.
5. Zaɓi sauke jakar baya domin hutawa yayin jira ko doguwar tsaiwa.
6. A zaɓi jaka mai aljihuna; a sanya abin da ke da tsini ko kaifi a aljihu mafi nisa da gadon baya. Sannan a sanya kayan da ke da nauyi a aljihu mafi kusa da gadon baya.
7. A ajiye kayayyakin da ba a buƙatarsu a gida domin rage nauyin jakar.
Idan kai ma'abocin rataya jakar baya ne kuma kana fama da ciwon wuya, baya, kafaɗa ko hannu, tuntuɓi likitan fisiyo a yau domin duba ka.
© Physiotherapy Hausa