TARIHIN GARIN PAWWA.
- Katsina City News
- 06 Nov, 2024
- 69
Pawwa, sunan wani Garin Dagaci ne a gundumar Kankara ta Jihar Katsina. Pawwa, tsohon Gari ne kwarai da Gaske, Yana daya daga cikin tsofaffin garuruwan dake Kasar Katsina. Ance zuruar wani mutum ne da ake Kira Muhammadu Yero Wanda aka fi Sani da " Kogo Mai-Kumaro" sune suka kafa Garin Pawwa a wajen Karni na goma Sha tara.
Kogo Mai Kumaro shahararren Mayakine, babu inda baa San shi ba a duk fadin Kasar Katsina da Zamfara. A cikin Karni na Sha tara ne (19th century) lokacin da Shehu ya fara Kiran da a kaddamar da Jihadi sannan a Jaddada addinin Musulunci, Sai Kogo Mai Kumaro ya shirya dashi da Jamaarsa yakai kansa wajen Shehu Mujaddadi, yayi masa mubayaa yace yazo ne ya bada gudummuwar da wajen Jihadi. Ana nan har Shehu ya gama Raba Tutoci, Amma Kogo Mai Kumaro Bai samu Tuta ba. Ance duk da haka ta tsata a wajen Shehu ya bada gudummuwar shi wajen Jihadi.
Ance bayan rasuwar Mujaddadi Shehu Danfodio a cikin shekarar 1817, Sai dansa Muhammadu Bello ya zama Sarkin Musulmi daga shekarar 1817 zuwa 1837. To a lokacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello aka Kogo Mai Kumaro Sarautar wani Gari da ake cema "Kurkutawa". Bayan rasuwar Kogo Mai Kumaro Sai dansa Abubakar ya gajeshi. Ance Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Yaba Abubakar Sarautar Kurkutawa da Mukamin Sarkin Gwari. Shi kuwa Garin Kurtukawa acikin wasu duwatsu yake. Da aka nada Abubakar Sai shi da Jamaarsa suka yanke shawara suka fita daga Garin Kurkutawa suka tafi wani Gari da ake Kira " Mai dorowa". suka zauna. A wannan Gari na Mai Dorowa ne Sarki Gwari Abubakar ya rasu.
Bayan rasuwar Abubakar Sai aka nada danuwasa Wanda ake cema Abdu da Gora Dan Kogo Mai Kumaro a Mukamin Sarkin Gwari. Shi bayan wani Dan lokaci ya yanke shawarar shi da mutanen da suka tashi daga Mai dorowa suka koma wani Gari da ake cema Wawar Kaza, suka zauna acan.
Bayan rasuwar Sarkin Gwari Abdu Kuma aka nada Halliru Dan Abubakar a matsayin Sarkin Gwari a shekara ta 1883. Baa Dade da nada sa ba, jamaar Garin suka nuna masa bukatar a Gina WA wannan Gari Masu Ganuwa don su Sami kariya daga abokan gaba idan an kawo Masu Hari. Sai Sarkin Gwari Abdu ya aika ma Sarkin Musulmi bukatarsu. To da Sarkin Musulmi Yaki haka, Kuma yaga Katsina tafi kusa da Wawar Kaza, to Sai ya aika ma Sarkin Katsina cewa ya ginama Mutanen Wawar Kaza Ganuwa.
Lokacin da Sarkin Katsina ya samu Wannan aike na Sarkin Musulmi Sai ya tura wani Bawansa da ake Kira Kunkuru, yace masa yaje ya ginama Mutanen Garin Halliru Ganuwa. Da Kunkuru ya Isa Garin ya Gan shi da girma Sai ya ga Lallai shi zai wannan aikin Sai yace kai wannan fili da girma yake PAWWA, kaji asalin sunan Garin Pawwa. Da aka gama ginin Ganuwar Sai mutane suka Rika Kiran Garin Pawwa Mai makon Wawar Kaza. Yanzu haka wannan suna ake Kiran Sarakunan wannan Kasa Wanda daga bisani suka tashi suka koma Kankara.
Ada can Pawwa Yana da wadansu kayan Sarauta na Gargajiya irinsu Tambura, da Wukar yanka, da Lifidi wadanda Sarkin Musulmi Yaba Kogo Mai Kumaro Kuma yayansa da jikokinsa sukayi gado har zuwa lokacin Sarkin Gwari Pawwa Halliru. Bayan rasuwar Sarkin Gwari Halliru Sai aka nada Abdu Dan Abubakar a Mukamin Sarkin Gwari Pawwa a shekara ta 1896. Yayi shekara goma Sha hudu Yana Sarauta.
Bayan rasuwarsa Kuma aka nada Sarkin Pawwa Bello Dabakurau Dan Sarkin Gwari Abdu da Gora acikin shekarar 1910. A zamanin mulkin Sarkin Pawwa dabakurau ne Turawa suka sake fasalin iyakokin Kasar Katsina da Sakkwato. Kafin Zuwan Turawa dai, Pawwa da Kankara duk suna cikin Kasar Sokoto ne, ita Kuma Kasar Yandoton Tsafe kuwa tana cikin Kasar Katsina. Amma da aka sake fasali, Yandoton Tsafe ta Koma Kasar Sokoto, Pawwa da Kankara Kuma aka maidasu Kasar Katsina. Wannan musayar Kasa da akayi Bai yima mutanen Pawwa Dadi ba, Sai Sarkin Pawwa Dabakurau yayi hijira daga Pawwa zuwa Sokoto.
Bayan da Sarkin Pawwa Dabakurau yayi Kaura zuwa Sokoto Sai Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada Nuhu Dan Iya Nadabo a matsayin Sabon Sarkin Pawwa a shekara ta 1915. Da Sarkin Pawwa Nuhu ya shiga Garin Pawwa Sai ya tarar mutanen Gari mafi yawansu sunyi hijira zuwa Sokoto wajan Sarki Dabakurau. Ganin haka Sai ya yanke Shawarar Maida Hedikwatar shi Kankara a maimakon Pawwa. Ya kwashe iyalinsa duka ya koma Kankara. Wannan dalilinne a komawar Masarautar Pawwa zuwa Garin Kankara, Kuma har yanzu anan Sarakunan Kasar Suke zaune har zuwa yau. An zagaye Garin da Ganuwa Kuma mutanen Garin sun Gina Gidan Sarauta.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.