Masarautar Bebeji a jihar Kano farkon Karni na Ashirin
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 631
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Fadar Sarkin Bebeji, dake kudancin Kano, a Arewacin Najeriya. Wannan gine-gine yana da sigar ginshiƙan gargajiya na Hausa, wanda ake samu a arewacin Najeriya.
Fadar da aka nuna a cikin hoton alama ce ta tsarin gine-ginen Hausa na gargajiya, wanda yake da ƙarfinsa a ginin tubali na laka da tsari mai kyau da kuma sauƙi.
Wannan hoto mai yiwuwa an ɗauke shi a farkon karni na 20, lokacin da Turawan Biritaniya suka mamaye Kano a shekarar 1903. Ganin sojojin mulkin mallaka na Biritaniya a wannan hoto yana nuna cewa an ɗauke shi ne a lokacin ko jim kaɗan bayan karɓar mulkin Biritaniya, wanda ke nuna zamanin mulkin mallaka lokacin da ƙasashen Turai suka mamaye yankuna daban-daban a Afirka.
Gine-ginen yana nuna fasahar maginan gargajiya na Hausa, wanda ya haɗa da:
- Ginshikin Tubali na Laka: Wanda ya zama gama gari a gine-ginen Hausa, yana bada kariya ta yanayi daga yanayin zafi.
- Ƙananan Ƙofofi da Tagogi: Wadanda aka yi don sarrafa iska da tsaro.
- Rufin Azara da Laka: Wadanan nau'in Rufi na gargajiya suna da amfani a yanayin riƙe ruwa a lokacin Damina da yalwar iska.
Bebeji, gari ne mai muhimmanci wajen kare hare-hare da kasuwanci daga kudancin Kano, a masarautar Kano.
Duk da haka, a lokacin mulkin mallaka, muhimmancinsa ya ragu yayin da hanyoyin kasuwanci suka canza, wanda ya haifar da raguwar huddatayyar kasuwanci da sauransu.
Mamayar Kano da Biritaniya da kuma mamayar garuruwa masu muhimmanci kamar Bebeji ya zama alamar canji a tarihin yankin. Zuwan Turawan mulkin mallaka ya haifar da canje-canje na gudanarwa da tattalin arziki wanda ya sake fasalin masarautun ƙasar Hausa da tsarin gargajiyarsu.
A takaice dai, hoton ba kawai yana ɗaukar kyan gine-ginen gargajiya na Hausa ba, har ma yana zama wata alama ta tarihi mai nuni da sauye-sauyen siyasa a lokacin mulkin mallaka a Najeriya.
Fadar Sarkin Bebeji (Hakimi) a yanzu ta zama shaida na sauyin zamani da al'adun gargajiya.
Don karin bayani na tarihi, duba rubuce-rubucen ilimi kan tarihin mulkin mallakar Biritaniya na Najeriya da gine-ginen gargajiya na Hausa.