SARAUTAR SARKIN MOTAR SARKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 15 Dec, 2023
- 861
Sarkin Mota shine shugaban duk wani direba na Masarautar Katsina. Sarkin Mota Yana gudanar da ayyuka kamar haka.
1. Tuka Motar Sarki
2. Tabbatar da Koda yaushe Motocin Sarki lafiya Lau suke garas.
3. Bada shawara ga Sabon direban da zaa dauka a Gidan Sarki.
Tarihi ya nuna cewa Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shine mutum na farko daya fara sayen Mota anan Nigeria ta Arewa tun shekarar 1913. Hakanan Kuma Alhaji Direban Sarki Dikko shine direban Farko na Nigeria ta Arewa ( first Driver in Northern Nigeria). Alhaji Ulu ya fara Tuki a shekarar 1913. Motar da Alhaji Ulu ya fara tukawa itace Sadly. Bayan rasuwar Sarki Dikko a shekarar 1944, Alhaji Ulu ya tuka Sarki Usman na tsawon wata ukku, sannan daga baya yayi ritaya, a cikin shekarar 1944. Ance akwai lolacin da wata matsala ta shiga Tsakanin shi Alhaji Ulu da Sarki Dikko. Sarki Dikko yasa Yari Hassan ya Kai Alhaji Ulu gidan Yari ya rufeshi, to ance tun daga wannan lokacin duk Motar dake Katsina, Sai da ta Kasa tashi. Koda yake a lokacin mutane kalilan keda motar a Katsina, daga shi Sarki Dikko, Sai Gidan Abu kyahi Kofar Saudi da sauransu. A lokacin Sai da Sarki Dikko yasa aka fiddo shi daga gidan Yari, sannan Motocin Katsina suka tashi suka fara aiki.
Bayan Alhaji Ulu yayi Ritaya Sai a koma N. A ta Katsina aka dauko wasu direbobi don hidimar gidan Sarki. A wannan lokacin an dauko direbobi kamar haka.
1. Alhaji Atti Gyare
2. Mijin Yawa
3. Na Umma Magajin Danko
4. Alhaji Labaran Zaria. Shine shugaban direbobin NA.
5. Alhaji na Hamza
6. Atu Guguwa.
Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ( 1944-1981) ya nada Labaran Zaria Wakilin Mota daga shekarar 1944 zuwa 1945.
Bayan Alhaji Labaran Zaria Sai aka nada Alhaji Ibra Dan Sarkin Makera ta bayan gidan Sarki Wakilin Mota, Mai kula da gyara Motar Sarki.
Direban Sarki Usman shine Alhaji Saidu Yar'adua, Mahaifin Senator Sadiq Yar'adua. Alhaji Musa Gadi Kofar SORO Yana taimaka Mashi , idan bayanan shike tuka Sarki Usman.
Bayan Alhaji Saidu yabar Tuki, sakamakon wata matsala Sai Alhaji Musa Sarkin Mota ya karba.
Alhaji Musa Sarkin Mota shine mutum na farko daya fara Sarautar Sarkin Mota. Ya fara tuka Sarki Usman a shekarar 1962, ya zama Sarkin Mota a shekarar 1987, lokacin Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman.
Bayan Alhaji Musa Sarkin Mota ya zama Sarkin Mota, Sai ya nemi izinin Sarki daya amince mashi wasu Sarautun Mota. Wadanda aka amince dasu sune.
1. Alhaji Inusa Dambo Wazirin Mota
2 Alhaji Sani Second Galadiman Mota
3. Alhaji Sani Kauran Mota.
Bayan rasuwar Alhaji Musa Sarkin Mota, Sai aka nada Wazirin Mota Inusa Danbo a matsayin Sarkin Mota. Shima Inusan Allah yayi Mashi rasuwa.
Hira da Sarkin Runbunan Sarkin Katsina Malam Alin Kanta.
Musa Gambo