"Mallam Dan Masani a kasar Katsina shi ya kirkiro Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa" ra'ayin Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano
- Katsina City News
- 02 Nov, 2023
- 910
Rubutun ajami, salon rubutu ne da Bahaushe ya samar daga harrufan Larabci. Wannan salon rubutu yana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun hanyoyin rubutu da aka yi amfani da ita a Ƙasar Hausa. Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), sun ce an haura sama da shekaru ɗari da hamsin ana amfani da wannan hanya ta rubutun ajami a Ƙasar Hausa kafin zuwan rubutun boko. Mashahuran malaman Musulunci na ƙarni na goma sha tara kamar irin su Mujadaddi Shehu Ɗanfodiyo da almajiransa, sun yi amfani da wannan salon rubutu wajen rubuta littattafai da waƙoƙi.
Farfesa Bunza (2002), ya fassara shi da cewa, “ajami na nufin rubutun harshen Hausa cikin harufan Larabci”.
Dangane da yaushe ne kuma a ina aka fara yin rubutun ajami kuwa, masana fannin Hausa sun yi rubuce-rubuce masu yawa kowa da nasa ra’ayin. Farfesa Bunza (2002), yana ganin cewa rubutun ajami ya wanzu a Ƙasar Hausa tun kafin zuwan Musulunci, ta in da ya kafa hujjoji da zuwan Bayajidda, da kuma dangantakar cinikayya da ta sarauta da ta wanzu tsakanin Ƙasar Hausa da kuma Ƙasashen Larabawa.
Shi kuwa Ɗanmasanin Kano, Alhaji (Dr.) Yusuf Maitama Sule, ya bayyana cewa malam Ɗanmasani na Katsina shi ne ya ƙirƙiro rubutun ajami na Hausa. A wannan ra'ayi nasa yau kenan ana lissafa shekarun ajami kusan shekaru ɗari bakwai kenan.
Sai dai, wani abu da ya fito fili shi ne cewa yaɗuwar addinin Musulunci a Ƙasar Hausa ta taimaka gaya wajen shaharar wannan salo na rubutu. Sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban rubutu a cikin harshen Hausa.
Wata 'Yar Wasiƙa Cikin Rubutun Ajami
أَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُ اللَّهِ تَعَالَى وَبَرَكَاتُهُ
مَلَمْ مُوْدِيْ يَ اِيَلِيْ؟ اِنَفَتَنْ كُوْمَيْ دَ كُوْمَيْ نَتَفِيَ دَيْدَيْ؟
بَيَنْ حَكَ، نَرُبُوتُو مَكَ وَنْنَنْ وَسِقَرْ دَنْ نَ تَمْبَيِ لَفِيَرْكَ دَ تَ اِيَلِنْكَ. سَنْ نَنْ كُمَ نَ تُنَتَرْ دَكَيْ مَغَنَرْ تَفِيَرْ مُ دَكَيْ ذُوَ عَيْكِنْ حَجِ دَغَ وَنْنَنْ وَتَنْ سَوْرَ وَتَ عَكَ. اِنَ فَتَ ذَكَ ذَمَ ثِكِنْ شِرِ، دَمُنْ ذُو غَرِيكَ وُثِي وَ ذَ مُي كَوَي بَ دَاكُو.
نَكَ أَلْحَجِ أَدُو.
Mun ciro wannan rubutun daga shafin Rumbun Ilimi