Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina yayi kira ga masu mu'ala da kafafen sada munta na zamani da gwamnati ta nada su kasance masu rubuta gaskiya
- Katsina City News
- 17 Mar, 2024
- 610
Mataimakin Gwamnan Alhaji faruq lawal jobe ya fadi hakan a ranar Asabar lokacin da Mataimakan suka kai mashi ziyarar ban girma a gidanshi dake tsohon gidan Gwamnati, a karkashin Jagorancin Hon Isah Mikidad, Babban Mataimaki na musamman akan kafafen Sadarwa na zamani na Maigirma Gwamna. Mataimakin Gwamna ya cigaba da cewa yaji dadin wannan ziyara da aka kawo mashi, kuma yana yaba irin kokarin da ake na tallata ayyukan Gwamnati, saboda haka nake kira agare ku da ku kasance duk abinda zaku rubuta kada ku kara kada kuma ku rage, haka kuma aikin ku aiki ne mai cike da kalubale to sai kun zama masu juriya da hakuri wajen isar da sakon Gwamnati ga al'umma, kuma kada kuyi fada da kowa , kada ku zagi wani ko cin fusakar wani , ku dai yi aikin ku na fadakar da al'umma akan ayyukan alkhairi da Gwamnati take yi, musamman irin nasarorin da Gwamnati ke samu akan harkar tsaro, abu ne mai kyau mutane su san wannan domin kara masu kwarin gwiwa.
Daga karshe yayi godiya da fatan alkhairi.
Tun a farko da yake jawabi , Hon Isah Mikidad ya bayyana ma Maigirma Mataimakin Gwamna cewa kamar yadda kake gani wannan tawaga ce ta mataimaka da Maigima Gwamnan Jihar Katsina ya nada su ashirin da biyar wandanda aka tura ma'aikatun Gwamnati daban daban domin su ruka bada bayanin irin ayyukan da Gwamnatin Maigirma Malam Dikko Umar Radda take a karkashin Ma'aikatun, kuma cikin yarda Allah dukkansu suna aikin su yadda yakamata, ya kara da cewa ranka ya dade, kwananan tsohon maitaimaka tsohon Shugaban Kasa Janar Muhammadu Buhari yayi wani rubutu cewa acikin sabbin Gwamnoni da aka zaba a 2023, ya zuwa yanzu wane Gwamna ne yafi kokari a Jiharshi, inda mafi rinjaye mutane suka zabi Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda Ph.D. wanda ko shakka babu wannan yana daga cikin tasirin bayyana ayyukan da Maigirma Gwamna yake yi ne a kafafen Sadarwa.
Kana tun da aka bamu wadannan mukamai babu inda mukaje, shi yasa muka ga dacewa muzo mu gaishe ka tare da neman shawarwari a matsayinka na jigo kuma uba .
Daga karshe muna maku fatan alkhairi , Allah ya baku ikon cigaba da ayyukan alkhairi domin ciyar da Jihar Katsina gaba.
Bashir ya'u
Media Assistant to katsina State Governor
Ministry for Basic and Secondary Education
16/3/2024.