Shugaban Bola Tinubu Ya Naɗa Jabiru Tsauri A Matsayin Kwamishinan Ƙasa Na NEPAD

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da naɗin Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri a matsayin Kwamishinan Ƙasa na hukumar NEPAD (New Partnership for Africa's Development). Wannan naɗin na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na tabbatar da shugabanci mai inganci da kuma karfafa ci gaban ƙasa a bangarorin haɗin gwiwa na kasashen Afirka.  

Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri mutum ne mai zurfin ilimi da gogewa a fannonin mulkin dimokuraɗiyya, hulɗar ƙasa da ƙasa, da harkokin majalisa. Ya kammala digirin digirgir na farko a fannin Harkokin Diflomasiyya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu ƙwarewa sosai kan yadda za a tafiyar da harkokin mulki cikin adalci da tsari.  

Tsauri ya kasance fitaccen jami’i a gwamnati, tare da ɗimbin gogewa a fannin gudanar da mulki da jagoranci. Ya na rike da mukamin Shugaban Ma’aikata na gidan gwamnati a Katsina kuma ya kasance amintaccen abokin aiki ga Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda (PhD). A matsayinsa na babban jami’i, ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Katsina, wanda hakan ya kara masa daraja da kima a idon jama’a.  

Naɗin Tsauri a matsayin Kwamishinan Ƙasa na NEPAD ya nuna yadda gwamnati ke ƙara mayar da hankali wajen ba da dama ga masu ƙwarewa don kawo ci gaba ga Najeriya da nahiyar Afirka baki ɗaya. Wannan naɗi na zuwa ne daidai lokacin da ake buƙatar ƙaruwar haɗin gwiwa tsakanin kasashen Afirka don magance ƙalubale da kuma samar da ci gaba mai dorewa.  

Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri dai an san shi da kishin ƙasa, dattaku, da kuma jajircewa wajen ciyar da ƙasa gaba, wanda hakan ya sa ake sa ran zai yi amfani da kwarewarsa wajen tabbatar da nasarorin da ake buƙata a NEPAD.