Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi
Rundunar Yansanda ta jihar Kaduna ta gabatar da wani yaro da a ke zargin an sato shi ne daga yankin Rafin Guza an Kuma sayar da shi ga wata Yar Kabilar Igbo a kan nera miliyan biyu.
Kakakin rundunar Yansanda na Kaduna, a cikin wani faifan bidiyo da su ka saki a Yanar Gizo, ya bayyana cewa, yaron Mai shekaru uku da haihuwa har an chanza ma shi suna zuwa Success David.
An samu nasarar gano yaron ne dai da taimakon wani kwararren Dan Jarida da ke aiki kafada da kafada da rundunar Yansandan ta jihar Kaduna.
Kamar yadda Kakakin na rundunar Yansandan ya bayyana, matar mai suna Florence Chibuzo yar asalin jihar Imo ce, wadda ta dade ta na koyarwa a jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewar Florence ta fara biyan kafin-alkalami na nera dubu dari biyu, kafin daga bisani ta biya cikon nera miliyan daya da dubu dari takwas ga wadanda su ka sato yaron.
Rundunar Yansandan ta ce a yanzu haka a na bin matakai tare da Hukumar makarantar da Florence ke koyarwa, don a Kore ta aiki kafin a gabatar da ita a gaban kotu.
Mai magana da yawun rundunar Yansandan ya yi kira ga iyaye a kan su zamo ma su sanya ido da kula kwarai a kan ya-yan su don kaucewa faruwar hakan.
Ya Kuma ja hankalin mutanen da ke son samun yara a kan su rika bin hanyoyin da doka ta tanada wajen daukar yaro a maimakon irin wannan aika-aika.