RUNDUNAR YANSANDAN JIHAR KATSINA TA KAMA MA SU GARKUWA DA MUTANE, TA GANO KUDIN FANSA NERA MILIYAN BAKWAI DA DUBU DARI BIYAR

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24052026_090156_FB_IMG_1779612880768.jpg

Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Jami'an Rundunar Yansandan jihar Katsina sun yi nasarar tarwatsa wani gungun ma su garkuwa da mutane su bakwai, in da su ka gano wasu daga cikin kudin fansa da sauran kayayyaki a hannun su.

Mutanen bakwai dai su ne a ke zargi da garkuwa da wani yaro Mai shekaru takwas a birnin Katsina.

Rundunar Yansandan ta bayyana cewa an yi nasarar cafke mutanen ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da Sabbin Jami'ai Na Musamman Na Yaki da Manyan Laifuka, watau  VCRU, su ka samu.

Kamar yadda Kakakin Rundunar Yansandan, Abubakar Sadik Aliyu, ya bayyana an yi garkuwa da yaron ne a ranar 13 ga watan Mayu, da misalin karfe shidda na yamma, a hanyar sa ta dawowa Islamiyya.

Ma su garkuwar sun tuntubi mahaifan yaron washegari, in da su ka nemi nera miliyan 50 kudin fansa don sakin shi.

Bayan an ja ciniki ne a ka bayyana cewa mahaifan yaron sun biya nera miliyan 17 kafin Sako yaron. Bayan samun rahoton lamarin, sai rundunar ta soma bincike in da a ka gano mutum shidda daga cikin ma su garkuwar a ranar Juma'a.

Wadanda a ka kama din sun hada da Nura Aliyu Mai shekaru 39 Wanda a ka bayyana a matsayin wanda ya kitsa aika-aikar kuma makwabcin mahaifan yaron, sai Abubakar Aminu mai shekaru 37 da Ibrahim Muhammad mai shekaru 51, sai Ilyasu Sani mai shekaru 51, gami da Abubakar Muhammad mai shekaru 27 da Kuma Abdullahi Ismail Mai shekaru 30.

Da a ka gudanar da bincike, wadanda a ka kama din sun amsa laifin su, in da su ka bayyana cewa akwai sauran Mutum guda Mai suna Abdul da ba a ka kama ba.

Rundunar Yansandan ta ce an samo binciken gano cikon Mutum guda din da ya gudu. Kayan da a ka samu sun hada da mota fijo samfurin 307 da Babur boxer, da nera miliyan bakwai da dubu dari biyar da a ke zargin wani bangare ne na kudin fansar.

Kwamishinan Yansanda na jihar Katsina Ali Umar Fagge ya yabawa jami'an a bisa wannan gagarumar Nasara da su ka samu.

Follow Us